SHUGABANCIN EFCC: Na shawarci Buhari ya nada Bawa saboda cancantar sa –Minista Malami

0

Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami ya bayyana cewa ya mika suna tare da shawarar Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Abdulrasheed Bawa, saboda cancantar sa kawai.

Malami ya bayyana cewa sunayen mutum hudu ne aka kai wa Shugaba Muhammadu Buhari, kuma cikin su har da sunan Bawa, domin a cikin su ya zabi daya ya nada shi sabon shugaban EFCC a lokacin.

A ranar 24 Ga Fabrairu ne dai Majalisar Dattawa ta amince da nadin da Buhari ya yi wa Bawa a matsayin sabon shugaban EFCC, bayan da Buhari ya bayyana sunan sa a ranar 15 Ga Fabrairu.

Sai dai kuma har yanzu ba a daina rade-radin cewa Malami ya yi ruwa-da-tsaki ba, wajen ganin cewa lallai an nada Bawa ya gaji korarren shugaban EFCC, Magu, wanda Malami ne sanadiyyar korar sa.

Banda masu cewa Malami ya dora Bawa ya kori Magu, wasu da dama kuwa na ganin cewa kwata-kwata dora Bawa a kan shugabancin EFCC bai ma dace da hankali ba, domin shi da ogan sa Malami duk ’yan jiha daya ne, wato jihar Kebbi.

Sai dai kuma a wata tattaunawa da Malami ya yi da Daily Trust, ya ce ba shi da wata alaka da Bawa, kuma dukkan masu kushe nada Bawa, ba su fito sun ce ba zai iya aikin da aka dora shi ba, sai dai a rika wasu surutan daban.

Daga cikin wadanda su ka nuna rashin goyon bayan nada Bawa, har da Babban Mashawarcin Buhari a bangaren Yaki da Rashawa, Itse Sagay, wanda ya bayyana kuru-kuru cewa Minista Malami zai rika yi wa Bawa katsalandan.

A rahoton wanda PREMIUM TMES HAUSA ta buga makonni uku da suka gabata, Babban Mashawarci kan yaki da rashawa na Shugaban Kasa, Itse Sagay, ya bayyana cewa ya jin tsoron lallai Ministan Shari’a Abubakar Malami ba zai bar sabon Shugaban EFCC, Abdulrashid Bawa ya yi aiki ba tare da ya yi masa katsalandan ba.

Malami wanda ya fito jiha daya da Bawa, shi ne ya haddasa musabbabin korar da aka yi wa tsohon shugaban riko na EFCC, Ibrahim Magu.

Har yau kuma Minista Malami din ne dai ya yi ruwa da tsaki aka nada Abdulrashid Bawa, wanda su ka fito jiha daya.

Sagay, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Mashawartan Shugaban Kasa a fannin cin hanci da rashawa, wato PACAC, ya bayyana a ranar Laraba cewa, a gaskiya bai gamsu da nadin da aka yi wa Bawa ba, saboda jiha daya ya fito da Ministan Shari’a, Abubakar Malami.

A cikin wata tattaunawa da jaridar PUNCH, Sagay ya ce akwai ma yiwuwar Bawa da Malami ‘yan uwan juna ne na kusa ko na nesa, tunda daga jiha daya su ka fito.

Sagay ya ce shi ya na magana ne bisa hujjojin da ya ke da su na katsalandan din da Malami ya rika yi wa EFCC a baya, ballantana kuma yanzu ga shi dan jihar sa ne aka nada. Sannan kuma da hannun Malami din wajen nada Bawa.

“Gaskiya bai kamata a ce Shugaban EFCC da kuma Ministan Shari’a duk su kasance sun fito daga jiha daya ba. Kuma zai iya kasancewa ma su na da kusanci na ‘yan uwantaka. Kenan Malami ba zai rika barin EFCC ta na gudanar da aikin kashin kan ta ba, ba tare da yi mata katsalandan ba.

“EFCC ba ‘yan siyasa ba ne. Amma shi Malami dan siyasa ne. Kuma ba zai rasa abokai da aminan masu kashi a gindi ba.

Sai dai kuma Malami ya bayyana cewa ba shi da dangantaka da Bawa, kuma ba Karamar Hukuma daya suka fito ba.

Malami dan Birnin Kebbi ne, shi kuma Bawa dan Jega ne.

Malami ya ce bai taba yin wata hulda da Bawa ba ta kusa ko ta nesa, duk kuwa da cewa a EFCC ya ke aiki.

Ya kara da cewa hazaka da kwazon Bawa da kuma kishin sa ne su ka sa ya cancanci zama sabon Shugaban Hukumar EFCC.

Share.

game da Author