Shin da gaskiya ne kasar Isra’ila ta kirkiro maganin da ke iya warkar da COVID-19 cikin kwanaki biyar? – Binciken DUBAWA

0

Zargi: Wani labari da wata kafar yada labarai ta wallafa na zargin cewa Isra’ila ta kirkiro wani maganin da zai iya warkar da cutar COVID-19 cikin kwanaki uku zuwa biyar.

Tun bayar bayyanar cutar COVID-19 daga Kasar Chana inda ta karade kasashen duniya da kuma yin ajalin mutane da dama bukatar samo maganin cutar ya zame wa kasashen duniya abin da za a maida hankali a kai domin dakile yaduwar cutar da yin ajalin mutane a sanadiyyar kamuwa da cutar.

Yarjejeniyar Isra’ila da Kamfanin Magunguna na Pfizer

Sakamakon nasarar da kamfanin Pfizer ya yi wajen samar da allurar rigakafi, akwai labarin da ya ce Isra’ila ta garzaya ta kulla yarjejeniya da Pfizern. Yarjejeniyar dai ta tanadi kamfanin Pfizer ya baiwa Isra’ila allurar rigakafin a yayin da ita kuma Isra’ilar ta yi alkawarin bai wa kamfanin magungunan wasu bayanan kiwon lafiya.

Ranar 11 ga watan Fabrairu aka kammala wannan yarjejeniya. Bayan da allurar rigakafin Pfizer ta isa Isra’ila, jarida Times ta kasar ta wallafa labarin cewa, rabin milliyan na al’ummar sun yi allurar daga daya daga cikin manyan asibitocinsu kuma babu wanda ya rasa ransa a dalilin allurar.

Zargin

Sai dai kuma jim kadan bayan wallafa wannan labari sai wani shafin yanar gizo mai suna worldtonewsng.com ya ruwaito cewa kasar isra’ila ta kirkiro wani maganin da ake shaka ta baki ta yin amfani da na’urar da ake kira inhaler a turance, wanda zai iya warkar da COVID-19 cikin kwanaki biyar. Wannan zargi ya kuma sake bayyana a shafin sada zumunta na Facebook, daga nan kuma aka sake wallafa shi a wani shafin labarai mai suna inspireradio.com da hujjoji iri daya da na labarin farko na worldtonewsng.com. Labarin ya kuma kara da cewa: “A Isra’ila, farfesa Nadri Aber ya kirkiro abun al’ajibi, wani maganin da mutun zai iya shaka ta baki ya warke daga cutar COVID-19 cikin kwanaki biyar kacal.

Wannan maganin na aiki kimanin kashi 96 bisa 100 saboda mutane 29 cikin 30, adadin wasu masu dauke da cutar da suka yi amfani da maganin a asibitin Sourasky da ke Tel Aviv sun warke. Sun shaki wannan maganin sau daya ne kawai suka warke, hatta wadanda cutar ta kama soasai an sallame su daga asibitin cikin kwanaki uku zuwa biyar.

Nadir da kan shi ya kwatanta maganin a matsayin “abun da ba’a taba gani ba” bayan da ya ga an sami sakamako mai gamsarwa. “Wannan na’ura sabuwar dabara ce aka yi, maganin cikinta kuma an inganta wasu kwayoyin da ake samu a jikin mutun ne wadanda aka fi sani da exomes a turance, da wasu kwayoyin CD4 da ake samu a jini. Da zarar mutum ya shaka, maganin zai zarce sai cikin huhu kai tsaye.”

Yayin da kwararru da masu binciken kimiya ke kokarin samun maganin da zai kawo karshen coronavirus, wannan labari, idan har ya kasance gaskiya zai faranta wa jama’a rai. Sai dai idan karya ne zai zama yaudara ce ga mutane su na amfani da maganin da ba ya aiki. Shi ya sa DUBAWA ta dauki nauyin bincikar gaskiyar wannan magana.

Tantancewa

Na farko DUBAWA ta sami tabbacin cewa lallai akwai wannan magani. Ana kiran shi EXO-CD24 wanda kuma farfesa Nadir Aber daga asibitin Sourasky a Tel Aviv ya kirkiro. Haka nan kuma tabbas an gwada maganin a kan mutane 30 kuma 29 sun warke tsakanin kwanaki uku zuwa biyar. Ma’aikatan lafiya kan bai wa mai dauke da cutar COVID-19 na’urar sanya maganin mai suna inhaler a turance, ya shaki maganin sau daya a rana, na tsawon kwanaki biyar.

Shi dai wannan EXO-CD24 ba warkar da COVID-19 ya ke yi ba, magani ne wanda ke inganta garkuwar jikin mara lafiya, ya kuma taimaka wa masu dauke da COVID-19 su dawo cikin hayyacinsu ko su farfado. Dr Shiran Shapira, shugabar dakin gwaje-gwajen kwayoyin halitta da ke asibitin Sourasky, kuma wadda ta dauki shekaru da dama tana nazarin kwayoyin da farfesa Arber ke bayani a kai ce ta bayar da wannan karin haske. Ta yi wannan bayani ne a wani bidiyon youtube lokacin da aka yi mata tambaya dangane da maganin.

Dr Shapira ta ce “maganin na rage zafin cutar a jikin wadanda suka kamu da COVID-19 kuma sukan yi amfani da maganin ne domin kada mara lafiya ya galabaita ta yadda ba sai ya bukaci taimako wajen numfashi ba ko kuma ma cutar ta kai ga mutuwa.

A cewar ta, idan har an riga an sa mai dauke da cutar a kan na’urar da ke taya numfashi, to an makara, dan haka, maganin ba ya warkar da cutar COVID – 19 yana taimakawa ne wajen rage yaduwar cutar a jikin mutum.” Ta kuma kara da cewa “Burinmu da wannan maganin ba kashe kwayar cutar ba ne, a wannan yanayin mun fi so mu inganta garkuwar jikin mutum ne yadda ba zai raunata sosai ba.”

Likitar ta ce maganin na matakin farko na gwaji ne saboda haka ba za a same shi a ko’ina ba yanzu sai an gwada shi a sauran matakai biyun da suka rage.

Sai dai bisa la’akari da hirar da aka yi da Dr. Shapira. Rahotannin da aka wallafa ba su da cikakken bayanin yadda maganin ke aiki.

DUBAWA ta sake tuntubar Dr Shapira domin karin bayani. Zamu bayyana cikakken bayani daga bakin ta nan ba da dadewa ba.

A Karshe

EXO-CD24 ba maganin warkar da COVID-19 ba ne. Sai dai ana iya amfani da shi wajen inganta garkuwar jikin wanda ya kamu da COVID-19 domin rage kaifin cutar. Saboda haka rahoton cewa Isra’ila ta kirkiro maganin da ke warkar da COVID-19 cikin kwanaki biyar karya ne.

Share.

game da Author