Shin da gaske ne ‘yan fashi sun tirke wasu ma’aikatan gidan man sannan suka yi awa uku suna sayar da mai a gidan man kamar yadda aka yi ta yadawa – Binciken DUBAWA

0

Wani mai amfani da shafin Twitter (@EjayOfLagos) ya wallafa hoton wata jaridar da ke dauke da labarin cewa wasu ‘yan fashi da makami sun daure ma’aikatan gidan wani man fetir sun kuma shafe sa’o’i uku suna sayar da man ga masu ababen hawan da ke bukata. @EjayOfLagos ya kuma kara da cewa “Labari da dumi-duminsa, wannan kasar ta zama tamkar barkwanci.” Irin kalaman da ‘yan Najeriya ke amfani da su kwanakin nan wajen nuna takaicinsu da yadda abubuwa ke gudana a kasar.

Wannan labari dai ya dauki hankali sosai a shafin Twitter, mutane 1,500 suka sassaka labarin, wasu 3,000 kuma suka sanya alamar yardada labarin sannan kuma batun ya sami martani 140 wadanda ke baiyana ra’ayoyi mabanbanta. Alal misali, wani mai amfani da shafin (@ayinde_uba) kalubalantar mawallafin labarin ya yi yana mai cewa “Wannan ba Najeriya ba ce, ku daina neman suna da jan hankalin jama’a dan su sake wallafa labaranku,” a yayinda wani kuma (@OverfeDamola) ya amince da labarin yana mai cewa “Ai ba inda wannan zai faru idan ba Najeriya ba. Shi kuwa (@horpeyemi) baiyana takaicinsa ya yi da cewa “Mu dai a cike muke da labarai masu ban dariya.”

Duk da cewa jama’a na da ‘yancin sanin abun da ke faruwa a kewaye da su, zargi irin wannan ka iya kawo rashin yarda, kuma al’umma ba zata rika amincewa da labaran ‘yan jarida ba. Shi ya sa DUBAWA ta yanke shawarar tantance wannan labarin.

Tantancewa

Daga farko dai, DUBAWA ta lura cewa allon da aka sanya farashin na man fetir, na dauke da alamar dala a maimakon nera. Wannan baya faruwa a Najeriya domin duk wani farashin mai da za’a sa a gidan man fetir, a nera ake sawa ba dala ko wata alamar kudi ta daban ba.
DUBAWA ta kuma gano cewa, wannan lamari tabbas ya afku amma ba a Najeriya ba. Ya afku ne a Zimbabwe a wani gidan man da ake kira Amakhosi, a daya daga cikin manyan biranen kasar mai suna Bulwayo wanda ke kan titi Victoria Falls.

Kafafen yada labarai a kasashen yankin kudancin Afirka, ciki har da Zimbabwe da Zambia sun dauki wannan labarin. Jaridar Zambian Observer ta yi amfani da kanun da @EjayOfLagos ya yi amfani da su wajen wallafa labarin a shafin Twitter Haka labarin ya ke a Iharere.com, wani shafin labarai na Zimbabwe. A shafin chorinicles.co.zw kuwa, jaridar ta dauki labarin tana amfani da kalaman da DUBAWA ta gani a shafin twitter.

Wani abun da ya kara sanya shakku akai shi ne yadda @EjayOfLagos bai bayar da karin bayani game da labarin ba, ko kuma ma adireshin shafin da ya sami labarin, domin wadanda za su so sanin cikakken biyani. Sai dai ya gina na sa labarin tare da hoton yana dangantawa da Najeriya.

A Karshe

Zargin cewa wasu ‘yan fashi da makami sun daure ma’aikatan gidan mai sun sayar da mai na tsawon sa’o’i uku ba gaskiya ba ne. Yunkuri ne kawai na yaudarar jama’a su ga kamar a Najeirya lamarin ya faru.

Share.

game da Author