Sai na fallasa sirrin da Babangida da ya binne a cikin kasa kan Abiola – Guru Maharaji

0

Jagoran Cocin ‘One Love Family’ da aka fi sani da Guru Maharaj Ji, ya yi alkawarin fallasa abinda ya faru tsakanin tsohon Shugaban Kasa na mulkin soja, Ibrahum Babangida, da kuma M.K.O Abiola, wanda ya yi nasara a vzaben 12 Ga Yuni, 1993.

Maharaji ya yi wannan bayani a cocin sa da ke Iju, Agege, a Lagos, kwanan nan.

Daga nan sai ya roki gwamnatin tarayya ta ta sake yin gyara ga tsarin bada dama ga masu fallasa wata harkalla ko babban laifi, domin su ji dadin fitowa su na tono wani abu da aka binne a karkashin kasa.

“Har yanzu wannan tsarin fallasa wadanda su ka saci kudin gwamnati su ka boye ko su ka sayi manyan mukamai da kadarori, bai samu karbuwa sosai a wurin jama’a ba.

“Mu na bukatar dokar musamman daga Shugaban Kasa cewa a rika bayar da kashi 20 bisa 100 na dukiyar da aka kwato a hannun barayin gwamnati ga wanda ya fallasa yadda aka kwato dukiyar, wato ‘whistle Blowers’, domin ta haka za a kara samun miloniyoyin mutane da yawan gaske Najeriya, yadda tattarin arziki zai bunkasa.”

Guru ya kuma yi kira ga gwamnati ta buga sunayen wadanda aka taba daurewa saboda sun saci kudin gwamnati, da kuma yawan kudaden satar da aka kwato a hannun kowane barawo.

“Sannan kuma a buga sunayen wadanda ake kan binciken su da wadanda harkallar su na kotu gaban mai shari’a, domin hakan zai taimaka a hana su yi wa binciken na su ko shari’un su katsalandan.

“Kuma a buga sunayen wadanda su ka yi wa gwamnati zube-ban-kwarya, su ka maida kudaden sata, aka fasa daure su.

“Kuma a kafa Dokar Musamman da za ta hana soja, dan sanda kai da sauran kowane jami’in tsaro karbar kudade kan titina daga hannun direbobin motocin sufuri.”

‘Buhari Ba Waliyyi Ba Ne’

Maharaj Ji ya bayyana Shugaba Muhammadu Buhari ba zai taba yin nasara ba, har sai ya yi nesa-nesa da tsoffin shugabannin kasar nan, irin su Babangida da sauran shugabannin da ke abokan sa.

Daga nan ya kara da cewa zai fallasa abinda ya faru tsakanin Abiola, matar sa Simbiat Abiola da kuma Babangida, lokacin Babangida ya taba kai ziyara gidan su a baya.

“Duk mai son haduwa da IBB musamman shugabannin da ke kai masa ziyara, su sani cewa ya na da wata kurwa wadda ba ta son ganin bakaken fata sun ci gaba a duniya.

“Idan kun tuna IBB ya sha rage wa ‘yan Najeriya martaba, shi ya sa mu ka samu kan mu cikin matsalolin da kasar nan ke ciki a yanzu.”

A karshe Maharaj Ji ya roki Buhari ya rika sa-ido a kan shugabannin da ke karakainar kai ziyara wurin IBB.

Share.

game da Author