Shugaban jam’iyyar APC na riko, gwamnan jihar Yobe, MaiMala Buni ya bayyana cewa jam’iyyar APC za ta yi mulki zango dai-dai har sau 10 kafin idan ma har wata jam’iyya za ta samu damar jin kamshin kujerar mulki a Kasar nan.
Buni ya fadi haka ne a wajen taron rantsar da mambobin kwamitin da jam’iyyar ta kafa domin tsarawa da shirya taron gangamin jam’iyyar da kuma yadda za ta tunkari zaben 2023 kuma ayi nasara.
Idan ba a manta ba Jam’iyyar PDP ta yi irin wannan barazana da kuri cewa sai ta yi shekaru 60 tana mulki a Najeriya kafin wata jam’iyya ta ji kamshin mulki a wannan kasa.
Sai dai kash, hakan bai yiwu mata ba, goguwar Buhari a APC ta yi mata kifa daya kwala.
Mala Buni, ya ce sai APC ta kafa gwamnati zango dai-dai har sau 10 kafin wata jam’iyya a kasar nan ta ji kamshi kujerar mulki.
A zantawa da yayi da manema labarai bayan taron jam’iyyar, gwamna jihar Jigawa Abubakar Badaru ya yi kira ga yan jam’iyyar su tsananta kishin su ga jam’iyyar.
” Mutane sama da miliyan 36 ne suka yi rajistan zama yan jam’iyyar APC a sabunta rajistar zama dan jam’iyya da APC ta yi a fadin kasar nan.
” Hakan nuni ne cewa yan Najeriya na nan tare da APC 100 bisa 100 kuma ita za su yi daga nan har sai in ta juya.
” Da farko mun buga kati 10,000 ne amma sai da muka kai ga buga katin zama dan jam’iyyar APC miliyan 36 ga shi har yanzu ana ce mana katin yayi kadan mutane sai roko suke yi a bugo sabbin katin rajista suma su tsunduma APC su ragargaji romo da lagwadar dimokradiyya da Buhari ke kwarara wa yan Najeriya sako-sako, ta ko ina a kasar nan.