RUƊANI: Shugabannin darikar Tijjaniya sun janye nadin Sanusi Lamido jagoran darikar a Najeriya

0

A wani bidiyo da Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi ya fitar ranar Lahadi da dare a Sokoto, ya karyata naɗin tsohon sarki Sanusi da kungiyar ta yi a wajen taron maulidi a Sokoto.

Da yawa daga cikin shugabannin jam’iyyar sun tabbatar da wannan nadi na Sanusi, Khalifan kungiyar, amma kuma jim kadan bayan samun karbuwa da karaɗe duniya da labarin ya yi wanda har abokanan sa irin su gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai sun mika sakon taya murna ga sarki Sanusi, sai kuma suka lashe aman su, suka janye nadin.

Ibrahin Dahiru Bauchi ya ce, kowa a kungiyar Khalifa ne na kungiyar ga mutanen sa.

A ranar Asabar ne illahirin shugabannin darikar Tijjaniya suka amince da nadin tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a matsayin sabon jagoran darikar Tijjaniya a kasar nan.

Kakan sarki Sanusi ne jagoran darikar Tijjaniya na farko a Najeriya. Bayan shi sai marigayi Isiyaka Rabiu wanda tun bayan rasuwar sa ba nada sabon khalifa ba.

Idan ba a manta ba an samu rarrabuwar kai a tsakanin mabiya daikar Tijjaniya a zamanin jagorancin marigayi Isiya Rabiu.

Darikar ta rabu kashi biyu, bangaren Isyaka Rabiu da kuma bangaren Babban malami Sheikh Dahiru Bauchi.

Kowane bangare na yin gaban kansa ne ba tare da yadda dayan su shine jagora ba.

Wannan nadi na sarki Sanusi ya kawo hadin kai a tsakanin mabiya darikar wanda ita ce darika mai yawan mabiya a kasar nan da Nahiyar Afirka.

Manyan malaman darikar Tijjaniya, daga kasashen Afirka da dama sun halarci wannan taron nadi a Sokoto.

Share.

game da Author