A ranar Talata ne Rigakafin Korona miliyan 4 suka iso kasar nan.
Shugaban kwamitin shugaban kasa kan dakile yaɗuwar cutar Korona a Najeriya Boss Mustapha, ministan Lafiya, Osagie Ehinare, da wasu s jami’an gwamnati ne suka tarbi isowar maganin daga kasar Indiya a filin jirgin dama na Abuja.
Da ma kuma tun a safiyar Talata, Mustapha ya shaida cewa Najeriya na da wuraren da za a jiye maganin ana yi wa mutane.
Sannan kuma ya kara da cewa gwamnati za ta saka ido domin kada a yi harkallar maganin wanda shine yanzu kwamitin za ta fi maida hankali a kai.
Ya ce za a saka jami’an tsaro, EFCC, ICPC da sauransu domin taya kwamitin sa ido kada a aikata ba daidai ba da maganin.
Bayan haka ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari da Mataimakin sa Yemi Osinbajo za su bayyana ranakun da za a yi musu rigakafin cutar a Talbijin din kasa kowa ya gani ya shaida.
Sannan kuma sai gwamnoni da manyan jami’an gwamnati don kowa ya shaida kafin kuma a ci gaba da yi wa sauran ƴan Najeriya.
Miliyan 4 ne ya iso zuwa yanzu, sauran za su ci gaba da zuwa a hankali, har a samu ayi wa kowa rigakafin.
Idan ba a manta ba tun a ranar Litinin ne Mustapha ya shaida cewa maganin zai iso Najeriya a yau Talata.
” Idan dai ba an samu wani tangarda ko jinkiri ba ne jirgin rigakafin zai ta so daga Indiya ranar Litini ya iso Najeriya ranar Talata.
” Muna sa ran daga wannan shekara zuwa 2022, za mu yi wa ‘yan Najeriya miliyan 70 rigakafin cutar Korona.
Korona a Najeriya
A ranar Lahadi ne aka samu mafi Karancin yawan wadanda suka kamu da Korona a Najeriya tun bayan barkewar cutar a karo ta biyu a Najeriya.
A cikin kwanaki 7 da suka wuce Najeriya ta samu karin mutane kasa da 700 da suka kamu da Korona. Mutum 341 ne suka kamu ranar Asabar.
Mutum 3 ne kacal suka mutu. Hakan ya nuna raguwa daga mutum 11 da suka rasu ranar Juma’a.
Hukumar NCDC ta bayyana cewa mutum 133,256 sun warke daga cutar cikin mutum 155,417 suka kamu a Najeriya.
An yi wa mutum 1,489,103 gwaji a kasar nan cikin ‘yan Najeriya akalla miliyan 200.