Kasar Austria ta bi sawun Afrika ta Kudu, inda ita ma ta yi watsi da rigakafin allurar AstraZeneca, wadda aka fara yi wa mutane ita daga ranar Lahadi a Najeriya.
Najeriya dai ta karbi kwalaben allurar AstraZeneca har milyan hudu, makonni biyu bayan da Afrika ta Kudu ta yi watsi da ita.
Afrika ta Kudu ta bayyana cewa ta yi watsi da AstraZeneca saboda masana kimiyyar kasar sun auna kuma sun yi gwajin da ya tabbatar masu cewa ingancin rigakafin ta wajen hana kamuwa da irin cutar koronar da ta addabi kasar, bai wuce kashi 30% bisa kashi 100% ba.
A ranar Litinin kuma sai ga wani sabon labari wanda ya tabbatar cewa Austria ta dakatar da yi wa al’ummar kasar ta rigakafin AstraZeneca biyo bayan mutuwar wata mata daya da kuma rashin lafiyar da ta kama wata matar, bayan an dirka masu allurar AstraZeneca.
PREMIUM TIMES ta tabbatar da wannan labari, wanda Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito.
“Ofishin Hukumar Kula da Lafiyar Jama’a na Tarayya na Austria ya samu rahoton wani akasin da aka samu ga wasu mata biyu, bayan an yi masu rigakafin AstraZeneca a asibitin Gundumar Zwettl.
“Wata mata mai shekaru 49 ta mutu sakamakon yi mata allurar AstraZeneca. Bincike ya nuna jinin matar ya koma mai yauki da kauri kuma ya na toshe hanyoyin magunanun jinin ta.
“Sai wata matar ta cikon biyu ita kuma mai shekaru 35, wadda ita kuma bayan an dirka mata allurar rigakafin AstraZeneca, sai huhun ta ya kumbura, magudanan hanyoyin da jini ke shiga da fita cikin huhun su ka toshe. Ita jinin na ta komawa ya yi mai kauri bayan an yi mata allurar. Amma ita wannan matar ta na samun sauki a halin da ake ciki.” Haka dai Hukumar Kula da Lafiya ta Austria, BASG ta bayyana.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda Afrika ta Kudu ta dakatar da allurar AstraZeneca, bayan ta rigaya ta karbi har kwalabe milyan daya da rabi.
A Najeriya dai ana ci gaba da yi wa wasu jami’an gwamnati allurar AstraZeneca, bayan da aka yi wa Shugaba Muhammadu Buhari da mataimakin sa Yemi Osinbajo, da kuma wasu jami’an kula da lafiya na tarayya a ranar Lahadi.
A ranar Litinin kuma an yi wa hadiman Buhari da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Ibrahim Gambari.