RIGAKAFIN KORONA: ECOWAS ta nemi a biya diyya ga duk wanda ya fuskanci canjin yana yi, nakasu ko tawaye a jikinsa bayan an yi masa allurar ‘AstraZeneca’

0

Kwamitin Sa-ido kan Rigakafin Korona a Afrika ta Yamma da Kungiyar ECOWAS ta kafa, ya nemi a biya diyya ga duk wanda bayan an yi masa allurar rigakafin korona, daga baya ya fuskanci wani canjin yanayin da ya haddasa masa wata rashin lafiya, nakasu ko tawaya a jikin sa.

Kwamitin ya ce yin hakan zai kara karfafa wa mutane da dama kwarin gwiwar yarda a yi masu rigakafin.

Babban Daraktan Hukumar Kula da Lafiya ta Afrika ta Yamma (WAHO), Stanley Okolo ne ya bayyana haka ta Taron Kwamitin Korona na 5 da aka gudanar karkashin REDISSE a ranar Asabar.

An dai gudanar da taron ne ta ‘virtual’, wato kowa ya gabatar da bayanan sa daga ofis, ta hanyoyin sadarwar zamani.

Okolo ya kara da cewa wannan bayani na sa wata matsaya ce kwamitin sun a Afrika ta Yamma ya dauka, kuma ya damka shi ga Kwamitin Ministocin Lafiya na Afrika ta Yamma, domin a zaburar da mutane da yawa su yi amanna da rigakafin ‘Covid 19’.

“Domin magana a nan dai ita allurar rigakafi ana kirkiro ta ne bayan an shafe kamar shekaru biyar ko bakwai ko ma takwas ana bincike. To yanzu an kirkiro wannan rigakafin korona cikin shekara daya, dole mu yi tunanin raba wa mutane diyya, idan har wani da aka dirka wa allurar ya samu wata matsala.” Inji Okolo.

Ya ce aikin COVAX da GAVI ne ganin an raba kwalaben allurar korona har bilyan biyu tsakanin kasashe 92 masu yawan marasa karfin iya sayen allurar a duniya.

Sai dai kuma Okolo ya ce har yanzu dai ba a samu rahoton wata matsala ba daga kasashen da ke ci gaba da gudanar da aikin rigakafin korona a cikin kasashen su.

Kwamitin da Okolo ke Shugabanta dai na gudanar da aikin sa a kasashen Afrika ta Yamma 1 da su ka hada da: Guinea, Senegal, Sierra Leone; Togo, Guinea-Bissau, Liberia, Nigeria; Benin, Niger, Mauritania, Mali.

Share.

game da Author