Tuni dai a safiyar Talatar nan lodin allurar rigakafin korona har kwalabe milyan 4 su ka iso Najeriya, ta filin jirgin saman Abuja.
Wannan allurar ta kyauta ce za a yi wa ‘yan Najeriya ita, daga Cibiyar COVAX, ba kudi Gwmnatin Najeriya ta ka ta sayo allurar ba.
Oxford/Astrazeneca ta na da arha, saboda tsadar ta bai kai kudin kwalbar barasa biyu ba.
An yi ittifakin cewa AstraZeneca ce daidai allurar da za ta karbi jikin mutanen kasashe masu tasowa. Sannan kuma wajen ajiya, za ta iya jure yanayin kasashe irin Najeriya.
Kasashe 92 marasa karfin tattalin arziki ne za a raba wa wannan allura kyauta a karkashin Cibiyar COVAX, wadda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi hadin-gwiwa da ita.
Najeriya ce kasa ta uku a Afrika da ta karbi rigakafin Korona na allurar AstraZeneca.
An bai wa Ghana kwalabe 600,000 sai Ivory Coast kwalabe 500,00 cikin makon da ya gabata.
Najeriya ce ta fi samun tallafin allurar rigakafin korona ta AstraZeneca, har kwalabe milyan 4. Ana kuma sa ran karin kwalabe milyan 12 su cika milyan 16 kenan nan ba da dadewa ba.
Daga ina aka kirkiro rgakafin AstraZeneca?
An kirkiro ta a Birtaniya, a wani kamfani ko masana’antar hada magunguna mai suna AstraZeneca, tare da hadin-gwiwar Jami’ar Oxford. An kirkiro ta ne a karkashin lasisin hada-magunguna na Cibiyar Serum da ke Indiya.
Ana sa ran samar da rigakafin AstraZeneca har bilyan biyu nan da 2024 a fadin duniya.
An debi kwayoyin cutar gwaggwon-biri ana hada kwayoyin cutar Korona, aka kirkiri rigakafin cutar korona ta AstraZeneca, wadda ke iya kare jikin mutum kamuwa da cutar korona. Wato allurar za ta zama garkuwar jiki kenan.
Me ya sa Afrika ta Kudu ta ki amincewa da rigakafin AstraZeneca?
Saboda allurar ta kasa yi magance cutar korona mai matakin 501Y.V2 a Afrika ta Kudu, sai kasar ta yi watsi da kwalabe milyan 1.9 da ta yi oda tun da farko.
Masana harkokin lafiyar Afrika ta Kudu sun ce rigakafin kashi 10 bisa 100 na cutar kawai ya ke iya warkaswa.
WHO ta shawarci Najeriya cewa tunda yanayin cutar koronar Najeriya ba irin ta Afrika ta Kudu ba ce, to za a iya amfani da AstraZeneca a Najeriya.
Ko kwalbar allurar AstraZeneca na da tsada?
Ba ta da tsada, kwalba daya ba ta wuce fam 2.5 na Ingila ba. Wato kusan kudin kwalbar barasa biyu kenan.
An yi gwajin cewa AstraZeneca na yin tasiri da kashi 76 bisa 100 ko sama da haka kadan. Amma Modanna ta fi ta aiki da kashi 90 bisa 10 ita na ta karfin.