Ministan Inganta Rayuwar Neja Delta, Godswill Akpabio, ya yi magana a kan mutanen da ba su da godiyar Allah, har su ke korafi da Shugaba Muhammadu Buhari a kan Matsalar tsaro a kasar nan.
“Ni fa ban ga dalilin da zai sa mutane su rika surutai suna cewa wai Fadar Shugaban Kasa ta yaudare su a kan rashin tsaro ba. Saboda mu na da ‘yan sanda, SSS da dukkan sauran bangarorin jami’an tsaro, wadanda kokarin da su ke yi ne ya sa har wasu masu korafin nan ke iya kwantawa da dare su yi barci.”
Akpabio ya yi wannan kakkausan furucin ne a wurin bude Hedikwatar Hukumar Bunkasa Yankin Neja Delta (NDDC) mai hawa 13 a Fatakwal, Babban Birnin Jihar Ribas, ranar Alhamis.
Sai dai kuma yayin da Akpabio ke bude hedikwatar, idan banda Gwamnan Imo Hope Uzodinma, babu wani gwamna dan yankin Neja Delta da ya halarci kwarya kwaryan bikin bude sabuwar hedikwatar, wadda Akpabio ya bude a madadin Buhari.
Dukkan jama’ar da ke wurin sun fahimci Akpabio ya rika jawabi ya ka muryar sa na rawa a lokacin da ya ke magana a wurin.
“Da ba Buhari ke mulki a kasar nan yanzu ba, to da jama’a ko barci ba za su iya yi a gidaden su da dare ba. Kai ko gwamna da barci sai ya gagare shi.” Inji Akpabio.
“Wasun su ba su tambaye mu abin da mu ke yi da kaso 13 bisa 100 na ribar danyen mai da ake bai wa wannan yanki na Kudu maso Kudu ba, amma saboda rashin kunya sai su bude baki su na gaya wa Shugaba Buhari maganganu na rashin mutunci.
“To ni ina so Shugaba Buhari ya yi watsi da duk masu maganganun nan marasa kan-gado.
“Ba fa wasu baki ba ne su ka lalata wannan wurin. An turo nairori tirilliyan, amma babu wani abu a kasa da za a iya cewa ga shi an yi da makudan kudaden, domin ci gaban yankin Neja Delta.” Inji Akpabio.
Sai dai kuma ba a san ko wane gwamna ne daga cikin gwamnonin Yankin Neja Delta Akpabio ke wa wannan harbin-iska ko zagi a kasuwa ba.
Sai dai kuma kowa ya san a duk fadin yankin Kudu maso Kudu, Gwamna Nysom Wike na Ribas ne kadai ke fitowa fili ya na ragargazar Buhari, ba tare da sarara masaba.
Akpabio dai ya yi korafin cewa shugabannin Hukumar Raya Yankin Neja Delta sun shafe shekaru ofishin ta na zaman haya, duk shekara sai dai a rika shirya makircin kwasar kudi da sunan biyan haya da sauran dabarun karkatar da kudade.
Akpabio ya gode wa Shugaba Buhari saboda irin kaunar da ya ke nuna wa Yankin Neja-Delta.