Wani rahoto mai tayar da hankali da Hukumar Kididdigar Alkaluma ta Kasa (NBS) ta fitar, ya nuna cewa kashi 33.3% bisa 100% na majiya karfi ’yan Najeriya ba su da aikin yi.
Wannan kididdiga da ‘National Bureau of Statistics (NBS) ta fitar na nufin a duk inda ka samu matashi uku, ko kato ma-ji-karfi uku, to daya daga ckin su ba shi da aikin yi.
Kididdigar dai har ila yau ta na nufin duk duniya kasa daya ce tal ta fi Najeriya yawan marasa aikin yi.
Fassara ta hudu da za a iya yi wa wannan bayanin kididdiga ita ce, rabon da Najeriya ta samu kan ta cikin dandazon yawan marasa aikin yi irin haka, bana shekaru 13 da su ka wuce kenan.
A takaice dai akwai mutum milyan 23.2 na marasa aikin yi a kasar nan.
Hakan kuwa na nufin cewa idan aka cire yawan cima-zaune, wato ‘yan kasa da shekaru 1 zuwa shekaru 14 da kuma ‘yan shekaru 65 zuwa sama, 50 daga cikin mutum milyan 69.7 masu karfin iya aiki, milyan 23.2 duk zaman kashe wando ko zaman dirshan ko zaman-jiran-gawon-shanu, ko kuma zaman ‘tammaham-ma-rabbuka’ su ke yi a Najeriya.
Rahoton ya kara yin bayanin cewa akwai adadin mutum milyan 122 masu karfin iya tashi su yi aiki a kasar nan, wato tsakanin dan shekara 15 zuwa ’yan shekaru 64.
Yawan su ya karu daga mutum milyan 117 zuwa 122 a cikin watanni uku na karshen shekarar 2020, wato Oktoba, Nuwamba da Disamba na 2020.
Rahoton ya nuna cewa akwai mutum milyan 69.7 tsakanin masu shekaru 15 zuwa 64 da za a iya cewa masu karfin iya yin aiki ne a Najeriya.
Daga cikin su kuwa masu shekaru 25 zuwa 34, wasu ajin majiya karfi, sun kunshi kashi 28.8 kenan.
Tsakanin watannin Oktoba, Nuwamba da Disamba, 2020, akwai mutum milyan 46.5 wadanda ke da aikin yi a kasar nan.
Idan aka bi diddigin jihohi kuwa, jihar Imo ce ta fi yawan marasa aikin yi a kasar nan, inda kashi 56.6 na majiya karfin jihar ba su da ikin yi.
Daga Imo sai mai bi mata jihar Adamawa da kashi 54.9, sai Cross River mai kashi 53.7.
A jihar Osun kashi 11.7 ne kadai marasa aikin yi, yayin da jihar Benuwai kuwa har kashi 43.5 ne ba su da aikin yau balle na gobe.
Jihar Lagos ce jihar da ta fi saura karancin marasa aikin yi da ke da kashi 4.5 kacal, sauran yawan majiya karfin jihar kuwa, duk su na da tudun dafawa a kowace rana.