Shugaban hukumar dakile yaduwar cutar Kanjamau na ƙasa NACA Gambo Aliyu ya bayyana cewa mata masu shekaru 20 zuwa 24 sun fi zama cikin hadarin kamuwa da cutar kanjamau fiye da maza da ke shekaru kamar haka a kasar nan.
Bayan haka kuma lissafi ya nuna cewa akalla mata kashi 1.3% ne ke dauke da cutar a Kasar nan wanda kashi 0.4% ne kawai maza.
Aliyu ya ce sakamakon bincike ya nuna cewa a cikin mata 10 akalla 6 na dauke da Kanjamau a kasar nan.
Sannan ya kara da cewa a wannan rana da ake bukin karrama matan duniya ya kamata a maida hankali wajen tabbatar da suna kaiwa ga samun kiwon lafiya mai nagarta da kuma wadata maganin Kanjamau ta yadda za su rika samu cikin sauki.
Sakamakon binciken da hukumar NAIIS ta fitar ya nuna cewa mutum miliyan 1.9 ‘yan ƙasa da shekaru 65 ne ke dauke da kanjamau a kasar nan.
A watan Disamba PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda maza dake luwadi suka fi zama cikin hadarin kamuwa da cututtuka musamman kanjamau fiye da mata masu yin madigo.
Wadannan rukunin mutane na cikin hadarin kamuwa da kanjamau ne saboda yadda suke saduwa ta dubura inda da dama daga cikin su basu amfani da kororo roba.
A Najeriya kwatan mazan dake harkan luwadi sun kamu da Kanjamau sannan da dama daga cikin su basu da masaniya ko kuma sun sani amma kuma sun boye haka saboda gudun kada hukuncin dokar hana luwadi ta hau kansu.