RANAR BARCI NA DUNIYA: Hanyoyi 8 da za a kiyaye don samun isasshen barci

0

Ranar barci na duniya rana ne da aka kebe don tunatar da mutane kan mahimmancin mutum ya rika samun barci yadda ya kamata.

Ana yin ranar tunawa da muhimmancin barci na duniya a duk ranakun 11, 12 da 13 na watan Maris.

Kungiyar likitocin kwakwalwa dake Amurka APA ta ce rashin samun issasshen barci kan haddasa hadarin mota, rashin iya yin aiki musamman a wurin aiki, samun matsaloli a soyayya da zamantakewa a tsanin mutane.

Rashin samun isasshen barci na kawo ciwon siga ‘diabetes’, cututtukan dake kama zuciya, damuwa da sauran su.

Kungiyar ta lissafi hanyoyin da za su taimaka wajen samun isashiyar barci.

1. A motsa jiki a lokacin da ya kamata kamar da rana ko safe amma ba lokacin da za a kwanta barci ba.

2. A guji shan giya da cin abinci a tsakiyar dare.

3. Idan za a kwanta barci a tabbatar cewa an samu wurin da bashi da yawan hayaniya ko kara.

4. Kada a yi hiran da ka iya tada hankali a lokacin da za a kwanta.

5. A zabi lokacin da za a rika yin barci da wuri.

6. A rage yawan yin barcin Rana.

7. A rage shan shayin dake dauke da sinadarin ‘nicotine da caffeine’

8. Kada a kwanta da damuwa a zuciya domin yin haka na hana samun isasshen barci.

Share.

game da Author