• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    Peter Obi ya fice daga PDP

    Peter Obi ya fice daga PDP

    TATTAUNAWA DA SARAKI:’Idan na zama shugaban ƙasa zan magance aringizon kuɗaɗen da ake yi wajen bayar da kwangiloli’

    Dino Melaye

    Dino Melaye ya sha ƙasa a zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP a Kogi

    EFCC ta cafke Okorocha bayan mamaye gidan sa da jami’an tsaro suka yi tun 11 na safe

    Dalilin da ya sa ƴan bindiga ke ci gaba da kai wa mutane hari a jihar Neja – SSG

    Yadda ƴan bindiga suka kashe mutum 11 a Zamfara a karshen makon jiya

    SHUGABAN ƘASA 2023: ‘Yan takarar APC na jihohin ƙabilar Igbo sun yi taron jiran-gawon-shanun goyon bayan duk wanda ya samu tikiti a cikin su

    TAKARAR SHUGABAN KASA: Muna tare da kai a koda yaushe – Sarkin Katsina Abdulmumini ga Osinbajo

    TA KICIME A APCn KADUNA: Ɓangaren Sha’aban ba su amince da zaben wakilan jam’iyyar APC da aka yi ba

    Yadda sojoji suka cafke gogarman masu garkuwa da mutane da wasu 150 a dazukan Zamfara da Katsina

    Askarawan Najeriya sun kashe ƴan bindiga 42, sun kama 20 sannan sun ceto mutum 63 da aka yi garkuwa da su – DHQ

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    CHAMPIONS LEAGUE: Ko dai tsinuwar Yaya Toure ta yi tasiri kan Pep Guardiola?

    PILLARS SUN KIRA RUWA: Daga yanzu a Abuja za su rika wasan gida kuma an zaftare musu maki 3

    Yadda Kanawa suka yi ragaraga da motar ƴan  Katsina United saboda Pillars ta buga kunnen doki a Kano

    GHANA vs NAJERIYA: Ko Najeriya za ta kauce wa ɗauko buhun kunya na 26 a hannun ‘Black Stars’?

    Barcelona ta yi wa Madrid dukan kabarin kishiya, ba sani ba sabo ta zura mata kwallaye 4 babu ko ɗaya

    ‘CHAMPIONS LEAGUE’: Yadda Benzama ya ceto Madrid daga rijiya gaba dubu, ya kori PSG kuma ya dawo da martabar sa a duniyar ƙwallo

    YAƘIN UKRANIYA YA CI ƘUNGIYAR CHELSEA: ‘Zan sayar da kulob ɗin na sadaukar da kuɗin ga tallafin waɗanda yaƙin Ukraniya ya kassara’ -Abramovich, mai ƙungiyar kuma ɗan asalin Rasha

    RASHA: FIFA da UEFA sun dakatar da ƙungiyoyin Rasha buga wasannin ƙwallon Turai da duniya baki ɗaya

    KYAUTAR NAIRA MILIYAN 2: Allah ya saka wa Ahmed Musa, ina kira ga ‘yan wasa na yanzu su yi tattali don gaba – Obiekwue

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    KURUNKUS: Malami ya fito takarar gwamnan Kebbi, ya ce jama’ar jihar ne suka tilasta masa ya fito

    2023: Ɗan takarar shugaban kasa, Rotimi Amaechi ya ziyarci masarautar Dutse

    LABARI CIKIN HOTUNA: Yadda ƴaƴan jam’iyyar APC da dubban mutanen Kaduna suka yi wa Sanata Uba Sani goma ta arziki

    BIDIYO: Shin zaka iya zama da mai dauke da cutar Kanjamau? – Ra’ayoyin mutane

    Dalilin da ya sa muka yi tattaki har Dubai domin taya Aisha Buhari murnar zagayowar ranar haihuwar ta – Matan Gwamnonin Najeriya

    BIDIYO: Yadda ‘yan bindiga suka rika jibga ta kafin a biya naira 50,000 kudin fansa – Dattijo Saidu Dabo

    ‘Yan mata marasa aure sun fi matan aure amfani da magungunan takaita Iyali – Ma’aikatar Lafiya

    BIDIYO: Kwalaben ruwan maganin rigakafin Korona sama da Miliyan daya da aka lalata a Abuja saboda sun gama aiki kafin a dirka wa ‘yan Najeriya

    BIDIYO: RIKICIN BILLIRI: Yadda muka rasa ‘yan uwa da dukiyoyin mu a rikicin sarauta – Galadiman Tangale

No Result
View All Result

PDP ta nemi a binciki wadanda su ka maka naira biliyan 797 a kwangilar titin Abuja zuwa Kano

Ashafa MurnaibyAshafa Murnai
March 30, 2021
in Babban Labari
0
TITIN ABUJA-KANO: Katsalandan din da Sanatoci suka yi mana ya sa aikin ke tafiyar hawainiya – Fashola

Jam’Iyyar PDP ta nemi a gaggauta sake tantance hakikanin kudin da aikin titin Abuja zuwa Kano zai lashi, wanda a farkon wannan wata, Shugaba Muhammadu Buhari ya amince za a kashe naira Billiyan 797.23 domin sake titin baki dayan sa.

Sannan kuma jam’iyyar har ila yau ta ki kira ga Hukumar EFCC ta tsunduma cikin bincike domin ta gano yadda aka yi azargagin makudan kudade a cikin kwangilar.

Haka kuma PDP ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya sa-ido sosai wajen tabbatar wa ’yan Najeriya cewa bay a tare da garken masu kokarin durkusar da kasar nan da ke cikin gwamnatin sa.

PDP ta ce wannan aiki da a baya ya ki ci ya ki cinyewa bayan an amince za a kashe naira biliyan 155 wajen gyaran titin, to ba abin amincewa ba ne ga mai hankali kuma yanzu a ce za a sake kashe naira biliyan har 797.23 domin a sake titin.

“Kawai dai gwamnatin APC ta kirkiro wata hanya ne da za a kwashe sauran naira biliyan 642 daga kwangilar a yi watanda tsakanin wasu shugabanni marasa kishin kasa da ke cikin wannan gwamnatin.”

Haka Kakakin Yada Labarai na PDP, Kola Ologbondiyan ya bayyana a cikin wata takardar da ya raba wa manema labarai a ranar Litinin.

“Wannan mahaukaciyar kwangila fa na nufin kenan gwamnatin Buhari za ta gina duk kilomita daya tal a kan naira biliyan 2.12.”

PDP ta bayyana cewa wadanda su ka zauna har su ka amince da kudaden kwangilar naira biliyan 797.23, sun raina wa ’yan Najeriya wayau, sun dauke su sakarkaru, shi ya sa ba su ji kunyar fitowa sun bayyana kudaden a idon duniya ba.

Daga nan sai PDP ta yi kakkausan kira a yi bincike kan kwangilar sannan a sake tantance adadin kudaden da za a kashe, dominn ko mahaukaci ba zai amince cewa duk a wajen aikin titin za a kashe har naira biliyan 797 ba.

Idan ba a manta ba, kwana daya bayan an bayyana kudaden kwangilar, PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin da sPDP ta ce akwai rufa-rufa da cuwa-cuwa a sabuwar kwangilar titin Abuja zuwa Kano.

“Kai jama’a! idan fa aka yarda cewa naira bilyan 797.23 za a kashe ta a titin Abuja zuwa Kano, mai tsawon kilomita 375, kenan za a dagargaje naira bilyan 2.12 a duk kilomita 1 kadai.”

Jam’iyyar PDP ta yi fatali tare kuma da nuna kin yarda cewa gaba dayan naira bilyan 797.23 duk a kan titin Abuja zuwa Kano za a kashe su.

Baya ga cewa kudaden sun yi yawan da ko mahaukaci sai ya yi mamakin yawan adadin kudaden, PDP ta ci gaba da cewa bayyana wadannan kudade a matsayin kudin kwangilar sake titin ya kara fito da irin munin harkalla, badakala, rufa-rufa da cuwa-cuwar da ke ci gaba da gunada a gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a karkashin jam’iyyar APC.

Wata sanarwa da Kakakin Yada Labrai na PDP, Kola Ologbondiyan ya fitar a Abuja ranar Lahadi, ya bayyana cewa, “Jamiyyar PDP ba ta na adawa ko nukura ba ne da irin ayyukan ci gaban da za a yi wa al’umma, musamman aiki mai muhimmanci kamar na titin Abuja zuwa Kaduna har Zariya zuwa Kano. PDP na magana ne a kan mahaukatan kudaden da aka ce wai duk a kan titin za a dagargaje su.

“PDP da duk wani dan Najeriya na mamakin irin makudan kudaden da aka ce za a kashe wajen sake gina wannan titi, wanda hankali da maras hankali ba zai iya amincewa da yawan adadin ba.”

Cikin makon jiya ne Gwamnatin Tarayya ta maida aikin titin daga gyare-gyaren da za a kashe naira bilyan 155 a kammala, ta bayyana cewa yanzu kuma bambare titin za a yi baki dayan sa, a sake sabo rangadau, amma kuma za a dagargaje har naira bilyan 797.23 a aikin sake gina titi, tun daga Abuja har Kano.

“Kai jama’a! idan fa aka yarda cewa naira bilyan 797.23 za a kashe ta a titin Abuja zuwa Kano, mai tsawon kilomita 375, kenan za a dagargaje naira bilyan 12.12 a duk kilomita 1 kadai.”

A kan haka ne sanarwar da PDP din ta fitar, ta nuna cewa matsayar ta a wannan kwangila shi ne an kirkiro ta ne kawai domin a karkatar da wasu makudan bilyoyin kudaden da ba a san adadin su ba, ta yadda za a sake tsiyata Najeriya, daga matakin tsiyata ta da ake a kan yi yanzu.”

Wannan kwangila dai yan Najeriya ba su da labarin cewa za a sake ta, kuma babu wanda ya ga lokacin da aka buga tandar neman‘yan kwangilar za su yi aiki, ballantana a auna cajin kudaden da kowane kamfani ya yi, a san wanda ya cancanta a bai wa aikin.

“PDP na kira ga ‘yan Najeriya su hankalta cewa titin Abuja zuwa Kano mai nisan kilomita 375, wanda za a kashe wa naira bilyan 797.23, kenan fa za a kashe naira bilyan 12.12 ne a kowane kilomila daya.”

Daga nan sai PDP ta bayyana cewa baya ga raina wa ‘yan Najeriya hankali da APC da kuma gwamnatin Buhari ta yi, wannan kwangila ta kara nuna yadda wasu shafaffu da mai ke cin amanar ‘yan Najeriya su na wawurar makudan kudaden talakawa wajen karyar gina titinan da babu mai mai tsarar irin su a fadin kasashen Afrika.

Sannan kuma PDP ta yi zargin cewa a asirce ake bayar da kwangilar, inda jami’an gwamnati ke yin rufa-rufa tsakanin su da ‘yan kwangila.

Akwai kuma zargin cewa wasu ayyukan gwangilar titinan ma ana bayar da su ne tun kafin kamfanin da aka bai wa kwangilar ya mika bayanan adadin kudaden da zai yi cajin a biya shi, kuma tun kafin ya tantance adadin tsawon titin ma dungurugum.

A makon jiya ne PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin cewa za a dagargaje naira bilyan 797.2 domin sake titin Abuja zuwa Kano baki dayan sa.

Rahoton dai ya nuna cewa titin Abuja-Kaduna-Kano da yanzu ake kan aikin gyaran wuraren da su ka lalace, yanzu kuma an ajiye batun gyara za a sake titin baki dayan sa.

A kan haka ne Gwamnatin Tarayya ta amince a kashe zunzurutun kudi naira bilyan 797.2 domin sabunta titin mai nisan sana da kilomita 400.

Minintan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola ne ya bayyana wa manema labarai na Fadar Shugaban Kasa wannan sabon aiki da za a tattago.

Ya ce an amince da sake titin baki dayan sa ne, a wurin taron Majalisar Zartaswa na Ranar Laraba, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta da kan sa a Fadar Shugaban Kasa.

A wurin taron kuma an amince a sayo motocin kashe gobara da wasu kayyakin da hukumar Kashe Gobara ke bukata.

Fashola ya bayyana cewa aikin gyaran titin Abuja zuwa Kano da a baya za a kashe wa naira bilyan 155 domin a kammala shi, yanzu zai ci naira bilyan 797.2, domin sabon titi garau za a gina gaba daya.

“Na gabatar da wannan bukata kuma an amince za a sake titin Abuja zuwa Kano gaba dayan sa. Ya tashi daga aikin gyare-gyaren wuraren da su ka lalace zuwa sake gina titin baki daya.

“Kenan kwangilar aikin ta tashi daga naira bilyan 155 ta koma naira bilyan 797.2

“Fashola y ace wasu titinan da aka kammala gyarawa kuma nan ba da dadewa ba masu kwangilar za su damka su ga Gwamnatin Tarayya, sun hada da titin Benin-Asaba, Abuja-Lokoja, Kano-Maiduguri, Enugu-Aba, Sagamu-Asaba, Kano-Katsina, Enugu-Fatakwal, Ilorin-Jebba da kuma Lagos-Badagary.

Sai dai kuma Fashola ya ce za a damka wa gwamnati titinan daya bayan daya.

Dangane da titin Abuja zuwa Kano, Fashola ya ce za a fara kammala Kaduna zuwa Zaria mai nisan kilomita 74. Ya ce shi ne za a kammala cikin 2022.

Sai kuma na Zaria zuwa Kano da Kaduna zuwa Abuja ya ce za a kammala shi cikin 2023.

Tags: AbujaAPCKadunaKola OlogbondiyanNairaNewsPDPPREMIUM TIMES
Previous Post

Shugaban karamar Hukumar Birniwa Jaji-Dole ya rasu

Next Post

Sojojin Najeriya za su kwankwatse duk wata barazanar da matsalar tsaro ke wa kasar nan –Janar Attahiru

Next Post
Karshen ’yan ta’adda ya kusa –Babban Hafsa Attahitu

Sojojin Najeriya za su kwankwatse duk wata barazanar da matsalar tsaro ke wa kasar nan –Janar Attahiru

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • Peter Obi ya fice daga PDP
  • Ba mu yadda mu janye wa mutum ɗaya ba, a shiga filin daga a fafata kawai – Ƴan takarar gwamnan Jigawa
  • AN YANKA TA TASHI: A biya ni naira miliyan 21 kuɗin fom ɗin takarar gwamna da na siya a PDP – Ɗan takarar gwamna
  • ZARGIN ƘARFA-ƘARFA A SIYASAR ENUGU: Sanata Ekweremadu ya saka takalmin ficewa daga PDP zuwa APC
  • TATTAUNAWA DA SARAKI:’Idan na zama shugaban ƙasa zan magance aringizon kuɗaɗen da ake yi wajen bayar da kwangiloli’

Abinda masu karatu ke fadi

  • Google on Masarautar Kano: Hassada Ta Sa Wasu Na Neman Wofintar Da Kokarin Su Danfodiyo! Daga Imam Murtadha Gusau
  • Kuşburnu Çekirdek Yağı on Dalilin da ya sa muka yi sallar Idi ranar Laraba a Bauchi, muka ki bin sanarwar Sarkin musulmi – Sheikh Dahiru Bauchi
  • Google on HARKALLAR BILIYAN 3.6: Ba nine Balan da ke jerin sunayen masu mallakin kamfanin Adda ba – Gwamna Bala
  • Google on SIYASAR ZAMFARA : Maitaimakawa tsohon dan takarar gwamna a APC akan harkar jarida ya sauya sheka
  • Google on RAMIN MUGUNTA: Yadda Boko Haram suka afkawa bam din da suka dana wa Sojojin Najeriya

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2022 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.