Jam’iyya mai mulki da jam’iyyar adawa, PDP sun yi tir da harin da aka kai wa gwamnan jihar Benuwai a gonar sa.
Gwamnan Benuwai Emmmanuel Ortom ya bayyana yadda wasu da yake zargi wai Fulani makiyaya ne sun kai masa hari a lokacin da ya kai ziyara gonar sa da sai da yayi gudun kilomita daya a cikin gonar a lokacin da ya ji harbin bindiga ta ko-ina.
Gwamnan ya ce sai da yayi gudun kusan kilomita daya a gonar kafin yayi iya arce wa maharan.
Jam’iyyar APC ta yi tir da wannan hari inda ta yi kira ga jami’an tsaro su gaggauta yin bincike akai domin kamo wadanda suka kai wa gwamnan hari.
Ita jam’iyyar PDP ta yi tir da wannan hari da inda ce lallai a gaggauta kamo wadanda suka fatattaki gwamnan daga gonar sa.
Haka kuma sufeto Janar din ‘Yan sanda ya aika da zaratan jami’an gudanar da bincike domin gano abinda ya faru da kuma bin diddigin wannan hari da aka kaiwa gwamnan a gonar sa.
A nashi jawabin gwamnan jihar Ribas, Nyesome Wike ya ce muddun aka kashe gwamnan Benuwai to shikenan ramuka biyu za agina da wanda za abizine gwamnan da kuma wanda za a bizine Najeriya ita kanta.
Gwamnan Jihar Benuwai vya saka dokar hana kiwo a jihar ba ki daya. Hakan ya sa a ‘yan kwanakinnan gwamnati ta kwace sanu sama da 200 da aka kama da laifin wai sun karya dokar jihar.