ZARGI: Wani rahoto daga jaridar Pulse Nigeria na cewa NAFDAC ta ce sam-sam allurar rigakafin AstraZeneca ba ta da hadari.
Da Najeriya ta fara bayar da allurar rigakafin AstraZeneca da ta karba ranar 12 ga watan Maris 2021. Mutane sun nuna rashin gamsuwarsu da allurar musamman bayan da hukumomin Afirka ta Kudu suka dakatar da amafani da ita.
To sai dai gwamnati da hukumomin lafiya sun cigaba da tabbatarwa jama’a cewa hadarin da ke tattare da allurar ba shi yawa kuma ana iya amfani da ita ba tare da an sami wani lahani ba. Illolin da akan gani irin wadanda dama can ba’a rasawa ne bayan an yi allurrar rigakafi.
Ana cikin haka ne Pulse Nigeria ta fitar da rahoton da ke cewa “COVID-19: Allurar rigakafin AstraZeneca bata da hadari- NAFDAC ta baiwa ‘yan Najeriya tabbacin haka.”
Hoton wannan labarin ya karade ko’ina wanda hakan ya sa DUBAWA ta bi diddigin fayyace gaskiyar maganar.
Tantancewa
DUBAWA ta sami wannan labarin ta karanta shi dan gano tushen labarin. Daga nan ne ta gano cewa ainihin labarin ya yi hannun riga da abinda NAFDAC ta fadi.
A cewar labarin, Babban darektar hukumar NAFDAC Mojisola Christianah Adeyeye, bayan da aka yi mata allurar rigakafin ta ce maganin na da hadari amma dai alfanun da za’a samu daga allurar ta fi hadarin da allurar ke tattare da shi.
“Adeyeye ta ce alfanun allurar rigakafin AstraZeneca ya fi hadarin da ke tattare da ita saboda an riga an gudanar da bincike. Ta ce babu magani ko allurar da ba ya tattare da hadari musamman a lokacin da ake kokarin kirkiro shi. Babban darektan ta ce bisa dukkan alamun da ke kwatanta ingancin allurar, alfanun ya fi hadarin yawa.” Bayanin Jaridar Pulse Nigeria.
A rahoton da jaridar Vanguard ta wallafa dangane da batun ranar 12 ga watan Maris 2021 ita ma ta wallafa dai dai iri rahoton Pulse amma kuma labarin ya banbanta ainihin labarin.
Sai dai a nata rahoton na ranar 17 ga watan Maris 2021 jaridar Guardian ta baiyana ainihin abinda darektar NAFDAC ta fadi, na cewa lallai akwai hadari amma alfanun ya fi yawa.
Dubawa ta kuma sake tuntubar kakakin hukumar NAFDAC Jimoh Abubakar sai dai wayarsa ta kasance a rufe. Dan hake ne aka tura mi shi sakon text aka nemi martanin shi dangane da batun inda ya amsa da cewa ba shi da abin da zai kara.
“Lalle, kun ji wakar daga bakin mai ita. Haka ya ki. Ba ni da wani abin da zan kara ko in rage.” … Amsar sakon text daga kakakin NAFDAC Jimoh Abubakar
Daga nan DUBAWA ta gudanar da bincike kan takardu da kasidu daban-daban dangane da allurar rigakafin AstraZeneca wadanda suka hada da na Hukumar Lafiya ta Duniya, Kungiyar Magunguna ta Turai da Hukumar kula da yaduwar cututtuka ta Afirka. Dukkaninsu sun nuna cewa duk da rahotannin daskarewar jini da sauran hadarurrukan da aka gani, alfanun sun fi yawa.
A Karshe
Gaskiyan magana dai shine, akwai rashin jin dadi a jiki da za aji idan aka yi allurar, sai dai kuma bayan haka ba za a sake jin komai ba. Alfanun sa ya fi rashin yawa.