Wani magidanci mai suna Jimoh Falola ya roki kotun gargajiya dake Ile-Tuntun a Ibadan ta warware aurensa da matar sa mai suna Opeyemi.
Falola wanda shine shugaban kungiyar ‘yan achaban jihar Oyo ya shigar da wannan kara ranar Talata yana mai cewa ba zai iya ci gaba da zama da Opeyemi ba saboda kama ta da ya yi da saurayinta turmi da tabarya a daki.
Ya ce ya auri Opeyemi shekaru 28 da suka gabata kuma ita ya fi so fiye da sauran matan sa 8.
” Duk da wadata gida na da komai na more rayuwa ashe cin amana ta takeyi da wani saurayinta tuntuni kafin asirin su ya tonu.
Shine ya sa gaba daya hankalina ya tashi, ganin ta da wani kato kwance a kan gado suna tabargaza.
Sai dai kuma matar bata karyata zargin ba, sai dai ta ce mijinta azzalimi ne, ta yi takaicin auren sa da ta yi har suka shekara 28 tare. In banda shan duka da nake yi da kwanan yunwa da ya’aya na babu abinda na ke samu gidan sa.
Alkalin kotun Henry Agbaje ya hori ma’auratan su kara hakuri da juna.
Agbaje ya bukaci ma’auratan su karo kwararran hujojji da za su gamsar da kotun sannan su gabatar da shedu ‘yan uwansu da za su tabbatar da hujojin da za su gabatar.
Za a ci gaba da Shari’a ranar 12 ga Afrilu.
Discussion about this post