A ranar Juma’a ne kotun gargajiya dake Mapo a Ibadan ta warware auren shekara shida dake tsakanin Abdulrasheed Olalere da matarsa Mariam.
Olalere ya kai kara kotu ne saboda matarsa Mariam da saurayinta na kokarin su gudu.
Ya ce ya kama mariam tana lalata da wani saurayinta bayan kuma tana dauke da cikin sa na wata hudu.
“Bayan Mariam ta haihu sai saurayin ya ce dan nasa ne.
Bayan gwaji da aka yi a asibiti, sai aka gano cewa dan sa ne ba na saurayin ba.
” Tana haihuwa bayan ta gama wanka sai kuma ta sake koma wa saurayin suka ci gaba da ganin juna har na gano suna shirya yadda za su gudu tare da saurayin.
Olalere ya ce akan wadannan dalilai ne ya bukaci kotu ta raba auren sa saboda ya hakura da auren.
Mariam bata ce komai ba game da zargin gudu da saurayinta da mijinta Olalere ya yi. Ta shaida wa cewa cewa rashin kula ne ya sa ta koma wa saurayinta, tunda shi na kula da ita.
Alkalin kotun Ademola Odunade ya raba auren sannan ya Bai wa Mariam nau’in kula da ‘ya’yan biyu.
Olalere zai rika biyan Naira 5,000 duk wata kudin kula da ‘ya’yan.
Odunade ya hori wadanda za su yi aure nan gaba da su auri wadanda suke so da wadanda suka amince da su.
Discussion about this post