MURNA TA KOMA CIKI: Boko Haram sun sake lalata wayoyin wutan lantarki a Maiduguri bayan gyara wadanda suka lalata a baya

0

Murna dai ta koma ciki ga mutane da mazauna garin Maiduguri jihar Barno, bayan sake lalata wasu manya-manyan wayoyin wutan tantarki a Maiduguri da Boko Haram suka sake yi ranar Asabar.

Idan ba a manta ba sai da aka dauki tsawon watanni akalla biyu babu wutan lantarki a garin Maiduguri saboda lalata wayoyin wutan Lantarkin da Boko Haram suka yi.

Ana zaune ne ciki duhu a duk tsawon wadannan watanni biyu babu wuta. Komai ya tsaya cak sai dai wutan Janareto. Harkokin kasuwanci sun tsaya,mutane sun shiga halin kakanikayi a garin Maiduguri.

Gwamnati da hukumar wutan lantarki na kasa sun yi kokari an gyara wayoyin da turakun da ke rike da su wanda suka sama bamabamai suka kada su kasa.

An xawo ana ta tika rawa da murnar dawowar wuta sai kuma a ranar Asabar suka sake saka waus bamabaman suka kada wasu turakun da ke rike da wayoyin wutana sannan suka rika harbin wayoyin da bindiga duk suka tsitsinke.

Yanzu dai gari ya koma dindim saboda wannan aika-aika da Boko Haram suka yi.

Wasu daga cikin ma’aikatan wutan lantarkin sun samu rauni sannan daya ya rasu a sanadiyyar taka bam da aka binne a karkashin kasa kusa da kafafuwan fol-fol din dake rike da wayoyin wutan lantarkin.

Yanzu kuma sai yadda hali ta yi.

Share.

game da Author