Hedikwatar Tsaron Sojojin Najeriya ta maida raddi dangane da wasu labarai da bidiyo da ke yawo a soshiyal midiya cewa Sunday Igboho ya kama wasu sojoji masu sintirin leken asiri a bayan gidan sa da ke Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.
Kakakin Hedikwatar Tsaron Sojoji, Bernard Onyeuko, ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai cewa, “sojoji ba za su taba zubar da ajin sub a, har su rika kwato ko labe-labe a bayan gidan wani mutum da sunan leken asirin sa ba.”
“Ya kamata kowa ya sani cewa sojojin Najeriya kwararru ne wadanda ke da cikakken horon duk irin aikin da za su gudanar a kasar nan. Kuma akwai iyakar ayyukan da ake dora masu da nauyin da su ka san ya ke wuyan su.
“Wannan nauyi kuwa duk ya danganci tsare kasa da kan iyakokin ta baki daya.
“Saboda haka sojojin Najeriya ba za su taba zubar da ajin su da kwarewar su wajen aiki ba, har su koma su na kwanto da labe-laben kokarin leken asirin wani mutum a bayan gidan sa.
“Saboda haka ba zai taba yiwuwa sojojin da aka tura aiki wai su buge su na lababe da kwato, kamar yadda ake yayatawa wasu sun yi a bayan gidan Adeyemo da ‘yan kanzagin sa ba.”
Sanarwar ta ce wanda aka kama ake zargi, ba soja ba, domin bincike ya nuna cewa mutumin ya sha yi wa sojoji sojan-gona.
Sanarwar ta kara da cewa ana ci gaba da bindike.
Discussion about this post