Minista Akpabio ya nesanta kan sa da farfesan da aka ɗaure saboda ya yi masa maguɗin zaɓe

0

Duk da shaidu kururu sun tabbatar da cewa Farfesa Peter Ogban da kotu ta daure saboda maguɗin zaɓe, ya yi wa Godswill Akpabio magudi ne a karkashin APC, Ministan na Harkokin Neja Delta ya ce shi bai ma san akwai wani Peter Akpan a duniya ba.

Kafin a nada Akpabio minista dai ya sake tsayawa zaben sanatan Akwa-Ibom ta Arewa-maso-Yamma a zaben 2019, amma dan takarar PDP Chris Ekpenyong ya kayar da shi.

Babbar Kotun Akwa Ibom da ke Ikot Ekpene ta kama Farfesa Ogban na Jami’ar Kalaba da laifin murde zabe a kokarin sa na ganin Akpabio na APC ya yi nasara.

Kotu ta same shi da bayyana sakamakon bogi na kananan hukumomi biyu, wato Oruk da kuma Etim Ekpo.

Daga nan aka daure shi shekaru uku a kurkuku ba tare da ba shi zabin ta raba. Sannan kuma a tuhuma ta biyu, aka umarce shi ya biya tarar naira 100,000.

Wannan shari’a ta na da dimbin tarihi, a matsayin ta na shari’ar farko da INEC ta fara daure gaggan masu magudin zabe.

Sai dai kuma Akpabio ya bayyana cewa ai shi ma ya ji dadin daure farfesan, domin shi ma ya maka masa kuri’un bogi.

Ya ce farfesan ya hada kai da Shugaban INEC na Jihar Akwa Ibom, Mike Igini su ka yi masa fashin kuri’u.

A zaben na 2019 dai sanatan PDP ne ke da rinjaye da kuri’u masu yawan gaske a lokacin kidaya, har sai daga baya aka rika angiza ruwan kuri’u ga Akpabio, wadanda Shugaban Zaben Jihar Mike Igini ya gano na boge ne farfesan ya cusa.

Dalili kenan INEC ta dakatar da bayyana sakamako, kuma ta ki bayyana Akpabio wanda ya yi nasara. A karshe dai nasara ta koma kan sanata dan takarar PDP.

Share.

game da Author