Matsalar tsaro ka iya hargitsa zaben 2023 –Gwamna Akeredolu

0

Gwamna Rotimi Akeredolu na Jihar Ondo, ya gargadi Gwamnatin Tarayya ta gaggauta daukar matakan dakile matsalar tsaro tun da wuri, idan ba haka ba kuwa, to za a iya fuskantar mummunan zubar da jini a zaben 2023.

Akeredolu, wanda kuma shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jihohin Kudu maso Kudu, ya yi wannan tsokaci ne kan tabarbarewar matsalar tsaro a wata tattaunawa da aka yi da shi a Gidan Talbijin na Channels, a ranar Talata.

Ya fara da buga misalin harin da aka kai wa Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai, wanda ya ce wannan kadai ya isa kowa ya gane cewa babu tsaro a kasar nan.

Yayin da ya ke ganawa da Shugaba Buhari a ranar Talata, ya yi gargadin cewa rashin tsaro ka iya hargitsa zaben 2023.

“Wato ni ina ganin cewa gaskiya ne ba za muiya gudanar da zabe a wannan halin yanayi na rashin tsaro ba kasar nan. Don haka idan ba a kawar da matsalar tsaron nan ba, to hare-haren ’yan bindiga zai karu matuka, ta yadda ba zai yiwu a gudanar da zabe ba, ko kuma a rika zubar da jini a lokacin zabe.

“To idan aka yi sake aka kai ga wannan mummunan yanayin da ba fatan kaiwa ake yi ba, wa ke ta wani zancen zabe kowa ta neman tsira da ran sa.”

“Saboda haka wajibin gwamnatin tarayya ne ta kawar da wannan matsalar tsaro domin kowa ya huta a kasar nan.”

Akeredolu kuma ya kara da cewa wannan matsalar tsaro ba za a iya kawar da ita dindindin ba har sai an kyale jihohi sun kafa yan sandan jihohi tukunna.

Share.

game da Author