Manyan dillalan fetur sun ki yarda a bar Matatar Dangote kadai ta fi kowa cin moriyar harkar mai a Najeriya

0

Kungiyar Manyan Dillalan Fetur da ake kira Major Oil Marketers Association of Nigeria (MOMAN), ta ce idan Matatar Mai ta Dangote Refinery ta fara tace danyen mai har ganga 650,000 a kullum, to ita kadai ce za ta rika cin moriyar harkar mai kenan a kasar nan.

MOMAN ta shawarci gwamnatin tarayya kada ta hana dillalan mai shigo da fetur idan har an kammala ginin katafariyar matatar mai ta Dangote Refinery.

Babban Sakataren MOMAN, Clement Isong ne ya bayyana haka ranar Alhamis a Lagos, lkacin wata hira da manema labarai.

“Duk da mun san akwai albarka mai tarin yawa idan aka bar wani kamfani ya narka jarin sa cikin wani gagarimin kasuwancin cikin gida, to duk dai da hakan, akwai fari da idan aka sakar wa wasu ‘yan kasuwa su rika cin wannan kasuwar.

“Don haka MOMAN ba ta goyon bayan a bar Dangote shi kadai ya rika cin karen sa babu babbaka a harkar shigo da albarkatun man fetur a kasar nan. Zai yi kyau a bar wasu su ma a dama da su, domin ita kasuwa ta mai rabo ce, amma ya kasance a kan ka’ida ya ke komai a kasuwancin mai a Najeriya.”

MOMAN ta dauki wannan mataki ne biyo bayan wani daftari da Dangote Refinery ya mika wa Gwamnatin Tarayya, cewa sai kamfanonin da ke da masana’antun tace danyen mai kadai za a bari su na rika shigo da mai a kasar nan.

A cikin daftarin shawarwarin da Matatar Dangote ta mika wa gwamnati, ta shawarci cewa a kasa wannan roko na kamfanin a cikin kundin kudirin Dokar Man Petur da ke ta hakilon kokarin tabbatar da kudirin zuwa doka.

’Yan Najeriya a dama na sukar wannan shawarar da Matatar Dangote ta bayar, a kan dalilin cewa idan har aka yi haka, to Dangote Refenery ce kadai za ta fi kowa cin moriyar hada-hadar danye da tataccen fetur a kasar nan.

Ita dai Matatar Mai ta Dangote Refinery, ana ci gaba da aikin gina ta ne a yankin Ijebu da ke Lekki, a Lagos.

Sannan kuma Isong ya kara da yin bayanin cewa su na kira kada a rika nuna bambanci wajen yanka farashin canjin kudaden waje ga wanda zai shigo da mai ko tace shi.

“Yanzu misali, tunda dai a duniya ana yanka wa gangar danyen mai farashi da dala ce, to nawa za a yanka wa dala farashi a kan musaya a naira?

Share.

game da Author