LEGAS: An yi wa mata 91 fyade cikin wata biyu –’Yan Sanda

0

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Lagos ta bayyana cewa ta samu rahoton aikata fyade har sau 91, cikin watannin Janairu da Fabrairu a cikin Legas.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Legas, Hakeem Odumosu ne ya bayyana haka sannan kuma ya ce an samu rahoton fadace-fadace tsakanin namiji da mace har sau 127.

Odumosu ya yi wannan bayanin ne a ranar Litinin, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai, inda ya sanar da su nasarori da ayyukan rundunar sa cikin watanni biyun da su ka gabata.

Ya kara da cewa baya ga cewa akasari baligai ne ake samu da aikata fyade, to amma an kuma samu rahotannin da kananan yara su ka yi wa karamar yarinya fyade a Lagos.

Kwamishinan ya kara da cewa an samu rahotannin aikata fashi da makami tare da kama ‘yan fashi sama da 200 a jihar Legas cikin watanni uku.

Kwanan baya PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda wasu yara su hudu su ka yi wa karamar yarinya fyade a Ejigbo, a Legas.

Yaran maza wadanda ba su wuce shekaru 16 ba dukkan su, sun yi wa wata karamar yarinya fyade ne a wani gida mai lamba 33, Titin Alhaji Obe da ke Ejigbo, wajen karfe 10 na dare, a ranar 18 Ga Fabrairu, 2021.

Haka kuma kwamishinan ya ce sun tura rigingimu ko wadanda aka zarga da aikata laifuka har 3,258 kotu a cikin watanni biyu, tsakanin Janairu da Fabrairu na wannan shekara.

Da ya koma kan masu fashi da makami kuwa, Kwamishinan ‘Yan Sandan Lagos y ace an kama mutum 234 duk wadanda ake zargi da aikata fashi da makai a cikin watanni uku a jihar Lagos.

Share.

game da Author