Kungiyar ‘Yan kasuwa masu siyar da kayan gwari da Dabbobi a yankin Kudancin Najeriya sun janye yajin aiki, bayan shafe kwanaki ba a shan jan miya a yankin

0

Kungiyar masu kayan gwari, wato Timatir, Albasa, Tattasai da shambo da atarugu, da na masu kasuwancin dabbobi ta ƙasa ta sanar da janye yajin aikin da take yi na dakatar da kai kaya a kudancin Najeriya.

Ƙungiyar ta janye yajin aikin ne bayan tattaunawa da wakilan gwamnatin tarayya karkashin jagorancin gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello.

Bayan amincewa ta janye yajin aikin Ƙungiyar ta mika wasu bukatunta guda biyar ga gwamnan domin gabatar da su ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari domin a biya musu.

Sai dai kuma kungiyar ta ce zata koma yajin aikin idan gwamnati ta yi watsi da bukutan su da suka amince da su a wannan ganawa da aka yi ranar Laraba.

Binciken da PREMIUM TIMES ta gudanar a garuruwan Lagos, Ibadan, Uyo, Abuja, Benin da sauran garuruwan kudancin Najeriya, ya nuna cewa farashin kayan abinci da naman shanu sai kara tsanani ya ke yi a wadannan garuruwa.

Wannan tashin gwauron zabo da farashin kayan abinci da na naman shanu a kudancin kasar nan, ya faru ne saboda yajin kai kayan abinci da Hadaddiyar Kungiyar Masu Safarar Kayan Abinci da Dillalan Shanu ke yi daga Arewa zuwa Kudu.

Ita dai wannan kungiya ta na neman diyyar naira bilyan 475 a matsayin biyan rayuka da dukiyoyin ‘yan Arewa da su ka salwanta a rikice-rikicen baya-bayan nan da su ka rika faruwa a kudancin kasar nan.

Share.

game da Author