Kotun Koli ta umarci Hukumar EFCC ta maida wa tsohon Babban Daraktan First Bank, Dauda Lawal kudin sa har naira bilyan 9 da ta rike.
Kotun wadda it ace kare-kukan-ka a Najeriya, ta yanke wannan hukunci a ranar Juma’a, inda ta jaddada hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke tun a cikin shekarar 2020, cewa a maida masa kudin sa.
Manyan Alkalan Kotun Koli biyar ne su ka yanke wannan hukunci, inda su uku su ka maince da hukuncin farko da Babbar Kotun Tarayya ta yanke, wanda kuma Kotun Daukaka Kara ta kara tabbatarwa.
EFCC ta rika daukaka kara ana kayar da ita, har zuwa Kotun Koli, inda a can ma kotun wadda ita ce ta karshe, ta ce EFCC ta maida wa Dauda Lawan kudin sa.
Tun a cikin watan Fabrairu, 2017 ne Mai Shari’a Hassan J na Babbar Kotun Tarayya ya umarci EFCC ta kwace kudaden daga tsohon Babban Daraktan na First Bank, har naira bilyan 9,080,000,000.00.
Tun cikin 2016 ne EFCC ta roki kotu aka kulle asusun ajiyar Dauda Lawan, bisa zargin cewa ya tara kudaden ta hanyar harkalla.
Cikin watan Oktoba, Babbar Kotun Lagos ta wanke Lawan, inda ta umarci kotu ta maida masa kudaden sa baki daya.
Bayan EFCC ta daukaka kara ne har zuwa Kotun Koli, a can ma ba ta yi nasara ba, inda a ranar Juma’a Kotun Kolin ta kwace kudaden daga hannun EFCC, ta ce a gaggauta maida wa Dauda Lawan kudaden sa.
Hukuncin ya na nufin EFCC ta bude asusun Dauda Lawan, wanda ta kulle tun cikin 2016, domin ya ci gaba da gudanar da sha’anin gaban sa da kudin sa.