Kotun Daukaka kara ta kori karar da APC ta maka Gwamna Obaseki na Edo

0

Babbar kotun Daukaka Kara ta Abuja, ta fatattaki jam’iyyar APC daga kotu bisa dalilin karar tankiyar zaben 2020 na Gwamnan Jihar Edo, wanda dan takarar jam’iyyar PDP, Gwamna Godwin Obaseki ya lashe.

Bayan korar karar da aka yi, Kotun Daukaka Kara ta kuma ci jam’iyyar APC tarar naira 250,000, matsayin kudin diyyar bata lokacin da kotun ta ce APC ta biya Obaseki, ladar jekala-jekalar da lauyoyin sa su ka rika yi a kotu.

Kotun ta ce babu wani dalili, hujja ko hurumin da APC za ta kai kara, domin ko ta wace fuska dai ta fadi zaben na jihar Edo.

Babban Mai Shari’a na Babbar Kotun Tarayya, Ahmed Mohammed tun a ranar 9 Ga Janairu, 2021 ya kori karar zargin Obaseki ya yi fajare na katin shaidar kammala Jami’ar Ibadan.

APC ta shigar da karar ce da nufin a kwace nasarar da Obaseki ya samu, a bai wad an takarar APC wanda ya zo na biyu, bisa dalilin zargin ta cewa Obaseki ya yi fojare na katin shaidar kammala jami’a ya damka wa INEC fojare na katin shaidar.

Mai shari’a ya fassara zargin katin shaidar fogare da aka yi wa Gwamna Obaseki da cewa abin al’ajabi ne matuka. “Tamkar wani bako ya zo gidan ka ya ce maka ba kai ne uban ’ya’yan da ka haifa ba.”

Yayin da APC ba ta gamsu da hukuncin wanda KotunTarayya ta Yanke ba, sai ta garzaya Koton Daukaka Kara, inda a can ma a ranar Alhamis kotun ta yi fatali da karar, tare da umartarv APC ta biya Obaseki diyyar naira 250,000 saboda bata masa lokacin da ta yi.

Da ya ke yanke hukunci, Mai Shari’a Stephen Adah ya bayyana cewa Kotun Tarayya ta yi daidai da ta kori karar, don haka babu wata bukatar sake daukaka karar har kotun sa.

Mai Shari’a Adah ya kara jaddada amincewar da Babbar Kotun Tarayya ta yi da shaidar da Magatakardar Jami’ar Ibadan, Abayomi Ajayi ya bayar cewa Obaseki ya halarci jami’ar cikin 1976, kuma ya kammala kwas din da ya je ya yi.

Ya ce shaidar da Ajayi ya gabatar ta tabbatar da cewa Obaseki bai yi fojare na sakamakon shaidar jami’a ya damka wa INEC ba, kamar yadda APC ta yi ikirari.

Share.

game da Author