Babbar Kotun Jihar Ribas da ke Fatakwal, ta umarci fitaccen mai magana a gidajen radiyo, Ifedato Olarinde, cewa ya biya diyyar naira milyan 5 ga mijin Benedicta Elechi, matsayin kudin danne fushin da mijin ya yi bayan ya kama Olarinde ya na lalata da matar sa.
An dai yanke wannan hukunci ne a ranar 18 Ga Fabrairu, 2021, kamar yadda jaridar PUNCH ta ruwaito, cewa zai biya kudin ga Paul Odekina, wanda a lokacin shi ne ke auren Benedicta, matar da Olarinde, wanda aka yi sani da Daddy Freeze ya yi lalatar da ita.
A kwafen shigar da kara mai lamba PHC/403MC/2012, Mai Shari’a Akpughunum ya yanke hukucin cewa a biya mijin naira milyan 5, domin ‘an shiga gonar sa an ci masa yabanya’.
“Sannan kuma kotu ta raba aure tsakanin Paul da Benedicta, saboda yawan kwartancin da ke tsakanin ta da farkan ta, Daddy Freeze, wanda aka ci tarar diyyar naira milyan 5.
Bayanan kotu dai sun nuna cewa rigimar dadaddiya ce, kuma an sha samun sabani ana rabuwa daga baya kuma a sasanta, tsakanin ma’auratan biyu, saboda yawan lalatar da matar ke yi ita da farkan ta Daddy Freeze.