Babbar Kotun Tarayya da ke Lagos ta bada umarnin a gaggauta sakar wa tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki dukkan kadarorin sa da EFCC ta sa kotu ta kwace a cikin 2019.
Wadannan kadarori da aka kwace dai duk gidajen sa ne da ke unguwar Ikoyi, a Lagos, wanda aka kwace a cikin 2019.
Mai Shari’a na Babbar Kotun Tarayya ta Lagos, Mohammed Liman, ya zartas da hukuncin cewa Hukumar EFCC ta kasa gamsar da kotu kwararan hujjojin da za su tabbatar wa kotu cewa ya sayi kadarorin ne da kudin gwamnatin Jihar Kwara, a lkacin da ya yi mulki a Jihar Kwara tsawon shekaru takwas da ya yi ya na gwamna.
Wannan hukunci ya biyo bayan lauyan Saraki mai suna Kehinde Oguwumiju ya rubuta cewa babu hujjar kama gidajen na wanda ya ke karewa. Shi ma lauyan EFCC Nnaemeka Omewa, ya rubuta wa kotu bukatar kwace gidajen.
A karshe sai Mai Shari’a ya bayyana cewa dama ma’anar kwace wa wanda ake tuhuma kadarori, ya na nufin kada ya yi gaggawar sayar da su kafin a yanke hukunci a kan sa.
Mai Shari’a ya ce EFCC ta rubuta wa kotun tarardar rantsuwa (affidavit) cewa, Saraki bai sa yi kadarorin da kudaden bashin da ya karba daga GT Bank ba.
To amma sai kotu ta bayyana cewa ta amince da matsayar da lauyan Saraki ya tirje ya tsaya a kan ta cewa, tilas sai EFCC ta gabatar wa kotu shaida da hujjar cewa da kudin bashin da Saraki ya ci daga GT Bank ya gina gidajen.
Don haka tunda EFCC ta kasa gabatar wa kotu hujjar cewa kudin da Saraki ya sayi kadarorin na sata ne daga cikin kudaden Gwamnatin Jihar Kwara, don haka babu wani dalilin da za a ci gaba da kwace kadarorin daga hannun Saraki.
Kotu ta ce hujjar da EFCC ta bayar a kotu, ba ta rasidin sayen gidan ba ce. Rasidi ne wanda aka yi bayan sayen gidan kuma huja ta nuna cewa da kudin bashin banki Saraki ya sayi kadarorin.
Mai Shari’a dai ya kori karar kuma ya ce a gaggauta bude masa kadarorin sa, wadanda EFCC ta sa wata kotu ta garkame a naya.
Discussion about this post