Kotun majistare dake jihar Legas ta daure wasu matasa biyu Kamolideen Baale, Mai shekara 28 da Tunde Tawa, mai shekara 26 a kurkuku bayan an kama su da laifin yin garkuwa da dan shekara biyar.
Alkalin kotun P.E. Nwaka ya yanke wannan hukunci ranar Laraba.
Nwaka ya ce Baale da Tawa za su ci gaba da zama a kurkuku har sai kotu ta kammala yin shawara da fannin gurfanar da masu aikata laifuka irin haka na jihar.
Za a ci gaba da shari’a ranar 16 ga Maris.
Bayan haka lauyan da ya shigar da karan Thomas Nurudeen ya ce Baale da Tawa sun yi awon gaba da dan makwabcin su da misalin karfe 8:30 na daren ranar 11 ga Fabrairu.
Nurudeen ya ce a wannan rana Baale da Tawa sun zolayi wannan dan makwabci inda suka ya biyo si dakin su za su aike shi. Yana shiga sai suka garkame kofar dakin suka hana shi fita.
Bayan iyayen yaron sun kawo kara ofishin ‘yan sanda ne aka fara farutar wadanda suka yi garkuwa da yaran har aka kama su.
Discussion about this post