Babban kotun sharia dake Kano ta bada belin Mahdi Shehu da ke tsare saboda fallasa harkallar biliyoyin naira da ake zargin gwamna Aminu Masari ya gabza tsakanin 2015 zuwa 2018.
Idan ba a manta ba, Kotu ta tsare Mahdi Shehu ne bayan gwamnan jihar Katsina Aminu Masari ya zarge shi da yi masa kazafi, karya da ci masa mutunci a kafafen yada labari inda ya zarge sa da gwamnatin Katsina da yin warwason wasu kudaden jihar Katsina dake ajiye a asusun bankunan UBA da Fidelity, daga 2015 zuwa 2018.
Mahdi ya yi wannan korafi ne a hira da yayi a tashar radio na Freedom sannan aka sassaka a shafukan facebook.
Hakan bai yi wa gwamnatin Katsina dadi ba ya sa ta maka shi kotu sannan aka ci gaba da tsare shi.
A zaman kotu a Kano ranar Alhamis, alkalin Kotun Mai sharia Ambrose Allagoa, yabada belin Mahadi akan naira miliyan 10, da kuma wani da zai tsaya mai kuma mazaunin Kano dake ka fili a Kano makamancin wannan tara na beli.
An rika yada wasu bidiyo a yanar gizo inda ake nuna Mahadi Shehu kwance kasa ya na rattaba salatuttuka da kalmar shahada, yana kwala wa shugaba Buhari kira ya zo ya cece shi da sauran kungiyoyin kare hakkin dan Adam su kawo masa dauki.