Kotu ta aika wa Malami, Emefiele, Magu da Falana sammacen zuwa yin bayanin yadda aka yi da kudaden da Maina ya tara wa gwamnati

0

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta amincce da bukatar tsohon Shugaban Kwamitin Garambawul din Hukumar Fansho, Abdulrasheed Maina, wanda ya roki kotu ta kira Ministan Shari’a Abubakar Malami, Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, domin su amsa tambayoyin kotu.

Sauran wadanda aka gayyata din bayan rokon da Maina ya yi, sun hada da tsohon Shugaban Rikon EFCC, Irahim Magu da kuma Lauya Femi Falana.

Mai Shari’a Okon Abang ya aika wa kowanen su sammace daban-daban, inda a ciki ya umarci da su bayyana a ranakun 9, 10, 11 da kuma 12 Ga Maris, domin su bayar da shaida.

Abang ya aika masu da sammacen bayyana domin bada shaida, bayan da Maina, wanda ake tuhuma da salwantar naira bilyan biyu ya nemi kotun ta yi haka.

Ana tuhumar Maina da karkatar da naira bilayn biyu daga cikin kudin fanshon ma’aikata.

Akalla sammace biyar Mai Shari’a ya aika wa mutane daban-daban, akasarin su manyan jami’an gwamnati bayan da Maina ya bukataci kotun ta kira su, domin su gurfana su bayar da shaida.

Sauran wadanda aka aika wa sammacen sun hada da M. Mustapha da ke Zenith Bank, Abuja, Mohammed Wakili tsohon kwamishinan ’yan sanda da kuma Keneth Amabem.

Akwai Kennedy Uzoka, Shugaban Bankin UBA, sai Nneka Onyeali-Ikpe, da Shugaban Bankin Fedility, sai Ibrahim Kaigama na NIPPSS, Jos da kuma Daraktan tabbatar da Bin Ka’ida na Babban Bankin Najeriya, CBN.

“Ana umartar ku da ku bayyana a wannan kotu mai lamba 6, ranar 9, 10 da 11 karfe 9 na safe, a wannan ranakun har sai gunadar da wannan shari’a wadda shi wanda ake tuhuma ne ya nemi ku zo ku bayar da shaida.

“Ku sani ana gayyatar ku ne a bisa madadi da umarnin Shugaban Kasa kuma Babban Kwamandan Askarawan Najeriya.”

Allura Na Neman Tono Garma: Dalilin Makalo Malami, Magu, Falana da ICPC Cikin Harkallar Maina:

Mai bayar da shaida a bangaren wanda ake kara domin kare shi, Ngozika Ihuoma ne ya ambaci sunayen su daya bayan daya a kotu.

Misali: Ihuoma ya yi ikirarin cewa Maina ya hadu da Malami da Mashawarcin Shugaban Kasa a Harkokin Tsaro a Dubai cikin 2016.

Ya ce “Maina ya bai wa Malami da Hukumar NSA wani rahoto na sirri, wanda ya yi sanadiyyar bankadowa da kwato wasu naira tiriliyan 1.3.”

Ya kuma yi ikirari a kotun cewa Kwamitin Fansho na PRTT a karkashin Maina ya kwato naira bilyan 282, wadanda aka ajiye a CBN. Wannan shi ne dalilin gayyatar Emefiele na CBN.

Sannan kuma mai bayar da shaidar kariya cewa Maina bai ci kudi ba, ya ci gaba da cewa an yi amfani da kudaden da Kwamitin Maina ya tara, inda aka ciri naira bilyan 74, aka zuba cikin kasafin kudin 2012.

Sannan ya kara da cewa Maina ya bai wa Hukumar ICPC rahoton sirri dangane da yadda ake kokarin karkatar da wata naira bilyan 35 daga ofishin tsohuwar Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Winifred Oyo-Ita.

Har ila yau, ya kara da cewa cikin watan Maris, 2013, Maina ya bayar da rahoton sirri ga Ministar Kudade ta lokacin, Ngozi Okonjo-Iweala da EFCC, har su ka kwato naira bilyan 15 daga Hukumar Kwastan, Hukumar Kula da Shige-da-fice har ma da Hukumar Fanshon Ma’aikatan Gidan Kurkuku.

Shi kuwa Magu, an gayyace shi ne saboda mai bada shaida a madadin Maina ya yi ikirarin cewa Kwamitin yi wa Hukumar Fansho Garambawul a karkashin Maina ta kwato kadarori 222 wadanda kudin su ya kai naira tiriliyan 1.63. Kuma duk ta damka su ga EFCC.

Ya yi zargin cewa EFCC da Magu sun yi kaca-kaca da kadarorin, inda aka yi watandar su ga wasu shafaffu da mai.

Shi kuwa fitaccen Lauya Falana, an gayyace shi ne saboda mai bayar da shaida, ya ce ya sayi daya daga cikin gidajen mai lamba 42, Gana Street, Maitama, Abuja.

Ya ce Falana ya mallaki gidan a lokacin da ake tsakiyar shari’a kan gidan.

Ihuoma ya ce an yi wa Falana gwanjon maka-makan gidajen da kudin su ya kai naira bilyan 6, amma aka sayar masa da su a wulakance, naira bilyan 1 kacal.

Sai dai Falana ya bayyana cewa shi bai sayi kadara ko kadarorin da ake tankiya a kan su ba.

Shi dai Ihuoma ya bayyana cewa ya bayar da shaida ne kawai bil-hakki da gaskiya, ba tare da an biya ko sisi ba.

Dalili, ya nuna cewa ai shi ya san komai, domin ofishin tuntubar sa mai suna Crincad & Cari Nigeria Ltd, ya yi wa Kwamitin Gyaran Fansho na Maina ayyukan tuntuba.

PREMIUM TIMES Hausa za ta kawon wa masu karatu yadda ta kaya a yau Laraba a zaman kotun.

Share.

game da Author