Kasar Denmark ta bayyana cewa rigakafin AstraZeneca ya kashe mutum daya, yayin da wasu mutane na kwance mutu-kwakwai rai-kwakwai a kasar.
A kan haka ne kasar tare da Sweden su ka ce sun a bukatar isasshen okacin sake nazarin rigakafin na AstraZeneca a kasashen na su.
Wadanda lamarin ya shafa dai jami’an asibiti ne, wadanda ciwo ya kwantar da su kasa da kwanaki 14 bayan an dirka masu rigakafin korona samfurin allurar AstraZeneca a asititocin Copenhagen, babban birnin kasar Denmark.
Wadanda aka yi wa allurar, ta kwantar da su ne bayan an yi masu ita, a matsayin maganin kamuwa da cutar korona.
Hukumar Kula da Ingancin Magunguna ta Denmark ta tabbatar da karbar rahoton mutum biyun da aka tabbatar na kwance dalilin toshewar magudanar jini da kuma lalacewar lakar cikin kwakwalwa.
Dama dai kasar Denmark ta dakatar da dirka wa jama’ar kasar allurar AstraZeneca tun a ranar 11 Ga Maris.
Baya ga Denmark, wasu kasashe kusan 15 mafi yawan su na Turai duk sun dakatar da yi wa jama’a rigakafin AstraZeneca , bayan bullar rahotannin cewa wasu da aka dankara wa allurar sun a fama da toashewar magudanar jini a cikin kwakwalwar su.
Hukumar Kula da Ingancin Magunguna ta Turai dai ta bada sanarwar cewa a ci gaba da dirka wa Turawa rigakafin AstraZenece, domin binciken da su ka gudanar bayan kasashe sun bijire wa rigakafin, ya nuna cewa allurar ba ta da wata illa.
“Idan ma ta na da wata matsalar, ba wani abin tayar da hankali ba ce, domin har gara a yi wa mutum rigakafin, ya da ce ba a yi masa ba.
Binciken wanda EMA su ka gudanar, ta yi nazarin mutum milyan 20 da aka yi wa allura a Ingila da sauran kasashen Tuarai wadanda su ka fara yin allurar, a kasashen kimanin 30, sun gano rahoton fuskantar matsala kan mutum bakwai kadai ta toshewar magudanar jini a cikin kwakwalwa, sai kuma matsalar CVST kan mutum 18.
Discussion about this post