A alkaluman da hukumar NCDC ta fitar game da Korona, mutum 48 ne kacal suka kamu da Korona ranar Litini.
Haka nan kuma an samu karin mutum daya da ya rasu a dalilin cutar duk a ranar Litinin.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Talata sun nuna cewa jihar Legas ta samu karin mutum 13, Kaduna-7, Nasarawa-7, Kano-6, Kwara-5, Ondo-4, Akwa Ibom-3 da Osun-3.
Yanzu mutum 162,641 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 150,466 sun warke, 2,049 sun rasu. Sannan zuwa yanzu mutum 10,126 ke dauke da cutar a Najeriya.
Rigakafin Korona
A ranar Lahadi ne hukumar NPHCDA ta bayyana cewa an yi wa mutum sama da 500,000 allurar rigakafin cutar korona a Najeriya.
Bisa ga bayanan da hukumar ta fitar ya nuna cewa an yi wa mutum 513,626 allurar rigakafin korona a jihohi 35 a kasar nan.
Shugaban hukumar NPHCDA Faisal Shu’aib ya ce har yanzu dai jihar Kogi bata fara yi wa mutanen ta allurar rigakafin korona ba.
Shu’aib ya ce hakan ya biyo bayan rashin samar da wuraren ajiye maganin rigakafin da daukan ma’aikatan da za su yi wa mutane allurar rigakafin da gwamnati bata yi ba.
Ya ce Jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda aka yi wa allurar rigakafin da mutum 110,042.
Daga nan sai jihohin Ogun-47,507, Kaduna-38,063, Bauchi- 32,482, Katsina- 28,918 da Kwara- 26,473.
Jihohin Abia-22, Taraba-111 da Kebbi-532 sune jihohin da suka fi samun mafi kankantan yawan mutanen da aka yi wa rigakafin korona.
Discussion about this post