A cikin kwanaki 4 da suka wuce Najeriya ta samu karin mutum 1,388 da suka kamu da Korona. Mutum 32 sun mutu.
Daga wancan mako zuwa wannan mako Najeriya ta samu ragowar mutum 15 da cutar ta kashe.
Hukumar NCDC ta bayyana cewa mutum 142,404 sun warke daga cutar cikin mutum 159,933 suka kamu a Najeriya.
Mutum 2001 sun mutu a dalilin kamuwa da cutar.
An yi wa mutum 1,601,396 gwaji a kasar nan cikin ‘yan Najeriya akalla miliyan 200.
Yawan mutanen da suka kamu a jihohin kasar nan ranar Alhamis.
Legas -107, Kwara -26, Akwa Ibom -23, Bauchi -22, Ogun -21, Rivers -19, Kaduna -14, FCT -11, Abia -8, Edo -8, Ekiti -6, Kano -5, Gombe -4, Osun -4, Oyo -3, Filato -3, Nasarawa -2, da Delta -1.
A ranar Talatan da ya gabata ne gwamnati ta karbi kwalaban maganin rigakafin cutar korona na AstraZeneca guda miliyan hudu.
Sannan a ranar Juma’a da ya gabata hukumar NPHCDA ta fara yi wa jami’an lafiya dake aiki a asibitin ƙasa dake Abuja allurar rigakafin korona.
Bayan haka shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo sun yi allurar rigakafin cutar ranar Asabar a fadar gwamnati.
Shugaban ƙasa Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su amince ayi musu allurar rigakafin cutar domin samun kariya daga cutar.
Bayan haka a ranar Litini ne shugaban hukumar NPHCDA Faisal Shu’aib ya bayyana cewa gwamnati ta fara raba wa jihohi maganin rigakafin cutar.
Ya ce gwamnati za ta aika wa jihohin maganin rigakafin ta jirgin sama sannan jihohin da basu da tashar jiragen sama za a kawo musu maganin rigakafin a mota.
Zuwa yanzu jihohin Kano, Jigawa, Maiduguri, Abia, Akwa-Ibom, Oyo, Osun, Ogun da Legas na cikin jihohin da suka karbi maganin rigakafin korona a kasar nan.
Discussion about this post