Masana’antar Rigakafin AstraZeneca ta ce babu hujjar cewa allurar na haddasa toshewar magudanar jini bayan an yi wa mutum rigakafin alluarar.
Kamfanin ya fitar da wannan bayani ranar da kasashen Ireland da Netherlands su ka bi sahun Austria da Afrika ta Kudu, su ka dakatar da dirka wa mutane rigakafin AstraZeneca.
“Binciken kwakwaf da mu ka gudanar ya nuna cewa babu wata hujjar da ke nuna cewa an samu wanda kokofin magudanar jinin sa sun kumbura, har jinin da ke bi ta magudanar ya na toshewa hanyoyin saboda jinin ya sauya ya yi kauri sosai.
“Mun yi wannan binciken mun tabbatar cewa babu wani jinsin mace ko namiji ko magidanci ko dattijo da ya fuskanci wannan matsalar ko a wace kasa.”
Binciken dai a cewar kamfanin sun gudanar da shi ne kan mutum sama da milyan 17 da aka yi wa allurar rigakafinkorona ta AstraZeneca, har da Birtaniya, daidai lokacin da kasashen Tarayyar Turai, irin su Irelands, Denmark da Norway su ka bada sanarwar dakatar da allurar maganin korona.
Mataimakin Babban Jami’in Kula da Lafiya na kasar Ireland, Ronan Glynn, ya bayyana cewa duk da dai babu wata nasabar matsalar toshewar magudanan jini da allurar rigakafin tukunna, to su na ganin dai gara su tsaida yin allurar, domin daukar matakai.
Ireland ta dauki matakin bayan da Norway ta bayar da sanarwar cewa an samu mutum hudu da magudanar jinin su ta toshe bayan an dankara masa allurar rigakafin AstraZeneca.
Ita ma Hukumar Kula da Magunguna ta Kasashen Turai a Hukumar Lafiya ta Duniya, ta ce babu wata hujja har yanzu da ke nuna cewa matsalar da aka bayar da bayani ko ta faru ne dalilin dirka wa mutum allurar AstraZeneca, mai maganin korona.
Cikin makon jiya ne dai PREMIUM TYIMES HAUA ta buga labarin cewa ECOWAS ta nemi a biya diyya ga duk wanda ya rika karkarwa, zabura ko shessheka, bayan an dirka masa allurar AstraZeneca.
Kwamitin Sa-ido kan Rigakafin Korona a Afrika ta Yamma da Kungiyar ECOWAS ta kafa, ya nemi a biya diyya ga duk wanda bayan an yi masa allurar rigakafin korona, daga baya ya fuskanci wani canjin yanayin da ya haddasa masa wata rashin lafiya, nakasu ko tawaya a jikin sa.
Kwamitin ya c yin hakan zai kara karfafa wa mutane da dama kwarin gwiwar yarda a yi masu rigakafin.
Babban Daraktan Hukumar Kula da Lafiya ta Afrika ta Yamma (WAHO), Stanley Okolo ne ya bayyana haka ta Taron Kwamitin Korona na 5 da aka gudanar karkashin REDISSE a ranar Asabar.
An dai gudanar da taron ne ta ‘virtual’, wato kowa ya gabatar da bayanan sa daga ofis, ta hanyoyin sadarwar zamani.
Okolo ya kara da cewa wannan bayani na sa wata matsaya ce kwamitin sun a Afrika ta Yamma ya dauka, kuma ya damka shi ga Kwamitin Ministocin Lafiya na Afrika ta Yamma, domin a zaburar da mutane da yawa su yi amanna da rigakafin ‘Covid 19’.
“Domin magana a nan dai ita allurar rigakafi ana kirkiro ta ne bayan an shafe kamar shekaru biyar ko bakwai ko ma takwas ana bincike. To yanzu an kirkiro wannan rigakafin korona cikin shekara daya, dole mu yi tunanin raba wa mutane diyya, idan har wani da aka dirka wa allurar ya samu wata matsala.” Inji Okolo.
Ya ce aikin COVAX da GAVI ne ganin an raba kwalaben allurar korona har bilyan biyu tsakanin kasashe 92 masu yawan marasa karfin iya sayen allurar a duniya.
Sai dai kuma Okolo ya ce har yanzu dai ba a samu rahoton wata matsala ba daga kasashen da ke ci gaba da gudanar da aikin rigakafin korona a cikin kasashen su.
Kwamitin da Okolo ke Shugabanta dai na gudanar da aikin sa a kasashen Afrika ta Yamma 1 da su ka hada da: Guinea, Senegal, Sierra Leone; Togo, Guinea-Bissau, Liberia, Nigeria; Benin, Niger, Mauritania, Mali
Discussion about this post