Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II, Wallahi Babu Abunda Hassadar Mahassada Za Ta Yi Maka Tunda Ka Rike Allah, Daga Imam Murtadha Gusau

0

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Assalamu Alaikum

‘Yan uwa masu girma, a gaskiya muna masu mika gaisuwar mu da godiyar mu ga Allah Ta’ala, tare da kuma da gode maku akan irin yadda kuka nuna, kuma kuka tabbatar muna da cewa kuna tare da mu a koda yaushe, dari-bisa-dari. Ina mai tabbatar maku da cewa sakonninku sun same mu, kuma mun karbi kiraye-kirayen da kuke ta yi muna a waya, illa kawai abun da zamu ce shine, Allah ya bar zumunci, kuma ya bar kauna da soyayya, shi kuma Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II, Allah ya kara masa hakuri, juriya, jajircewa, da karfin imani, amin.

Alhamdulillahi, muna kara godewa Allah, da ya kaddari a yau, duk duniya ta fahimci cewa, duk wannan abu da ake yiwa Mai Martaba, Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II, ba komai bane illa cutar hassada daga makiyansa. Allah cikin ikon sa yasa al’ummah ta fahimci wannan, kuma ta gane gaskiyar abun da ke faruwa. Wannan ba karamar baiwa bace da Allah Ta’ala yayi muna. Muna gode masa akan wannan.

Domin a duk lokacin da ake zaluntar ka, kayi hakuri, kuma al’ummah tana kallon cewa kai mutum ne barrantacce daga duk sharrin da ake kokarin dangana maka, kuma ake kallon wanda yake zaluntar ka din a matsayin shine azzalumin, sai ka godewa Allah akan wannan.

Yadda lamarin yake shine, duk wani mai yi maka hassada baya so yaga kafi shi, baya so yaga kaci gaba, baya so wani alkhairi ya same ka, baya so yaji an yabe ka, kullun so yake yi yaji an zage ka, ko an bata ka, ko an aibata ka, ko an tono wata kasawarka. Idan ka samu wani abun alkairi zai aibanta abun, ta yadda mutane ba zasu kimanta shi ba. Kuma shi kullun, so yake yi wani abu na sharri ya same ka, sai ya ji dadi, yayi murna, yayi farin ciki.

Sannan Ya Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II, wallahi abu ne sananne a wurinka cewa, mahassada ba zasu taba kyale ka ba, domin duk wanda Allah yayi wa ni’imah, ko wata baiwa, to dole sai ya samu mahassada, sai dai duk da haka akwai hanyoyin da addininmu na Musulunci ya kawo, kuma Malamai suka bayyana muna, wadanda suke hana hassadar yin tasiri a gare ka. Ya Khalifah, ka san su wallahi, sai dai in tunatar da kai na, da masoya, sannan kuma in yi gargadi ga makiya. Ga wadannan hanyoyi kamar haka:

1. Neman tsari a wurin Allah daga sharrin masu hassada, da magauta, da makirai, da makiya. Ya Khalifah, wallahi muna da tabbacin a koda yaushe, tsaye kake akan wannan!

2. Sanya tsoron Allah da kiyaye umarninsa da dokokinsa, domin wallahi, duk wanda ya kiyaye Allah, to Allah zai kiyaye shi. Shi ma wannan ko makiyanka sun shaide ka akan wannan Ya Khalifah!

3. Yin hakuri akan abun da abokin gaba yake yi maka; ma’ana, duk abun da suke yi kar ya dame ka. Sannan kar mu ce zamu rama mummunan abun da suke yi muna da mummunan aiki irin nasu, domin in har ba mu rama abunda suka yi muna ba, to tabbas Allah zai rama muna. Amma fa mu sani, ina ta sake nanata wa, cewa, ba laifi bane mu tashi tsaye domin kare kan mu daga sharrinsu, tare da fayyace gaskiya domin mutane su fahimce ta, da kuma tona asirin makiya! Don haka, mu ba zamu zalunci kowa ba, ba zamu yiwa kowa sharri ba, amma tabbas, ko shakka babu, wallahi, zamu ci gaba da daukar duk matakan da suka dace domin kare kan mu, domin mun fahimci cewa babu Allah a tare da su!

4. Mu ci gaba da zama masu karfin dogaro ga Allah, Allah yana cewa a cikin Suratu Dalak, ayah ta uku, cewa:

“Duk wanda ya dogara ga Allah, to (Allah) ya isar masa.”

Idan ka dogara ga Allah, sharrin mahassadi ba zai taba cutar da kai ba, ko da kuwa ka ga wani abu da yake na cutarwa ne a taka fahimtar, to wallahi, wallahi, wallahi karshensa zai zama alkairi a gare ka, da dukkan jama’arka, da masoyanka, da mabiyanka.

5. Fuskantar Allah Madaukakin Sarki, da tsarkake aiki zuwa gare shi (Ikhlasi), da yawan ambatonsa (wato Zikr). Wannan ma sai dai mu kara zage damtse akan wanda muke yi!

6. Tuba daga zunubai, domin ba za’a dora maka wani ya rin ka cutar da kai ba, sai idan akwai wani zunubi da ka aikata, kana sane da zunubin ko baka san shi ba. Ko kuma ya zamanto an yi wannan ne domin a jaraba karfin imaninka a gani. Bamu shakkar ka Ya Khalifah akan duk wadannan!

7. Yawaita yin sadaka, da kyautatawa bayin Allah, da yawaita yin alkhairi, gwargwadon iko, kuma iya abun da zaka iya. Saboda wallahi yana da wahala Allah ya dora mai hassada akan wanda yake kyautatawa mutane. Ya Khalifah, wallahi Ilahirin Kanawa, da ‘yan arewa, da ‘yan Najeriya kafatan, Allah ya sani, suna sane cewa kai mai alkhairi ne, kai mai yawan kyauta ne, don haka sai dai ince a kara, ko kuma aci gaba da yi.

8. Kyautatawa wanda yake yi maka hassadar. Sai dai na san wannan yana da tsananin wahala matuka. Amma dai abun nufi a takaice shine, idan makiyi yabi mummunar hanya, ta haram, wadda Allah ya hana, domin ya yake ka, to kai kuma sai kabi duk hanyoyin da suke Allah ya yarda da su, domin ka kare kan ka daga sharrinsa da makircinsa!

Sannan babban maganin cutar hassada da kuma neman tsari daga gare ta shine; mutum ya kasance mai wankakkiyar zuciya, mai yarda da hukuncin Allah a koda yaushe, kuma a kowane yanayi ya samu kansa.

Haka kuma ana so mutum ya yawaita yin addu’oi da rokon Allah. Makiyanka da masu yi maka hassada ba kwanciya zasu yi ba, zasu iya bin duk wata hanya, ko wace iri ce, kuma komai muninta, domin ganin cewa sun durkusar da kai, sun gama da kai, an daina jin labarin ka gaba daya. Da ma labarin naka ne basu son ji, ganin ka ne ma basu son yi kwata-kwata a cikin wannan duniyar. Wanzuwar ka cikin wannan duniya barazana ne a wurinsu, idan kana motsawa, basa iya bacci, kuma basu samun kwanciyar hankali. Don haka kar muyi wasa da addu’a da rokon Allah Ya Khalifah.

Sannan idan muna tsoron cutarwa daga wani mutum, ko muna fuskantar hassada ko cin mutunci daga gare shi, ko daga Jama’arsa, to ga addu’ar da zamu karanta domin samun kariya daga Allah. Wadda muka samu kai tsaye, daga Manzon Allah (SAW). Kuma In Shaa Allahu, duk wata mummunar aniyarsu zata koma kan su in Allah yaso. Ga addu’ar nan kamar haka:

“ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺭَﺏَّ ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﻭَﺍﺕِ ﺍﻟﺴَّﺒْﻊِ، ﻭَﺭَﺏَّ ﺍﻟْﻌَﺮْﺵِ ﺍﻟْﻌَﻈِﻴﻢِ، ﻛُﻦْ ﻟِﻲ ﺟَﺎﺭﺍً ﻣِﻦْ ‏(ﺍِﺳﻤُﻪ) ﻭَﺃَﺣْﺰَﺍﺑِﻪِ ﻣِﻦْ ﺧَﻼَﺋِﻘِﻚَ، ﺃَﻥ ﻳَﻔْﺮُﻁَ ﻋَﻠَﻲَّ ﺃَﺣَﺪٌ ﻣِﻨْﻬُﻢْ ﺃَﻭْ ﻳَﻄْﻐَﻰ، ﻋَﺰَّ ﺟَﺎﺭُﻙَ ﻭَﺟَﻞَّ ﺛَﻨَﺎﺋُﻚَ، ﻭَﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻟَّﺎ ﺃَﻧْﺖ.”

“Allahummah Rabbas-samawatis-sab’i, wa Rabbal-Arshil-Azim, kun li jaran min (Sai ka ambaci sunansa anan), wa ahzabihi min khala’iqika, an yafruta alayya ahadun minhum au yatgha. Azza jaruka, wa jalla thana’uka, wa la ilaha illa Anta.”

“Ya Allah, Ya Ubangijin Sammai bakwai! Ya Ubangijin Al’arshi mai girma! Ina rokonka, Ka zama Mafaka a gare ni daga sharrin wane (Sai ka ambaci sunansa anan) da shi da jama’arsa da tawagarsa daga cikin halittunka. Kada wani daga cikinsu yaci mutuncina, ko yai cutarwa a gare ni. Mafakarka ta buwaya, kuma yabonka ya daukaka. Kuma babu abin bautawa da gaskiya sai Kai.”

Ya Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II, kar ka damu da hassadar masu hassada. Wallahi wannan ba zata cuce ka ba, matukar ka ci gaba rike Allah. Shi Allah din zai isar maka.

Ya Mai Martaba Sarki, daga lokacin da ka fahimci cewa wane ba ya kaunarka, ko kuma wane yana yi maka hassada, to kai kar ka yi masa sharri, kar ka rama abinda yake yi maka, amma dai ya zama dole, kuma ya zama wajibi ka tashi wurin kare kan ka, daga sharrin makiya da masu hassada, wannan ba laifi bane, kai hasali ma, abu ne da yake tilas, domin umurni ne daga Allah da Manzonsa!

Ya mai daraja Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II, ka sani cewa kyautatawa zuwa ga masu yi maka hassada, yana kara maka daukakar daraja ne a wurin Allah. Sannan kuma yin hakan zai zama garkuwa a gare ka daga sharrinsu.

Sannan ita hassada guba ce, kuma cuta ce wadda take saurin halakar da masu yinta, tun kafin ta shafi wanda aka yi dominsa. Don haka idan ka kyale mahassada da halinsu, sharrinsu ma ya ishe su zama bala’i, da dawwama cikin damuwa. Shi yasa Allah ya umurci Annabinsa (SAW) cewa, ya nemi tsari daga sharrin mai hassada yayin da yake hassadarsa.

Ya Allah ka kiyayemu daga sharrin mahassada, da makirai, da magauta, da matsafa, da bokaye, da ‘yan bori, da miyagu, albarkacin hasken Alkur’aninka, amin.

Idan har muka kiyaye wadannan, to ina da cikakken yakinin Allah zai ci gaba da taimaka muna In Shaa Allahu, kamar yadda har kullun yake taimakon mu.

Wassalamu alaikum,

Dan uwaku, Imam Murtadha Muhammad Gusau ya rubuta daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.

Share.

game da Author