Karshen ’yan ta’adda ya kusa –Babban Hafsa Attahitu

0

Babban Hafsan Askarawan Najeriya, Ibrahim Attahiru, ya bayyana cewa yaki da ‘yan ta’addar da ake yi Najeriya ya kusa zuwa karshe, inda Najeriya za ta yi gagarumar nasara a kan Boko Haram.

Attahiru ya bada wannan tabbaci a Damaturu, Babban Birnin Jihar Yobe, yayin da ya ke jawabi ga sojojin Sashe na 2 na ‘Operation Lafiya Dole’, inda ya jinjina masu dangane da gagarimar nasarar da su ka yi, inda su ka yi kwatsa-kwatsa da wasu ’yan ta’adda.

“Ina matukar farin ciki da lafahari da ku. Saboda kwamandojin ku sun shaida min irin bajintar da ku ka yi baki dayan ku.

“An shaida min yadda ku ka yi bajinta wajen fatattakar Boko Haram a farmakin ‘Operation Tura Ta Kai Bango’ da ku ka yi masu.

“Ina matukar alfahari da ku. Kuma na tabbata cewa a ci gaba da sake fatattakar da za ku sake yi masu, za ku kara kaimi sosai, ta yadda za a kawo karshen wannan masu ta’addancin baki dayan su.” Inji Attahiru.

Ya shaida masu cewa ya je wajen su ne domin ziyarar gani da ido, tsakanin sa da su kowa ya san juna. Sannan kuma ya sanar da su cewa Shugaba Muhammadu Buhari na gaishe su, tare da jinjina gare su baki dayan su.

“Ina dauke da gaisuwa ta musamman daga Shugaba, kuma Babban Kwamandan Askarawan Najeriya, Muhammadu Buhari. Ya na sane da irin kokarin da ku ke yi, da nuna kishin kasa a cikin sadaukarwa.

Sabon Babban Hafsan Sojojin dai ya yi wannan furucin cewa an kusa dakile Boko Haram, makonni uku bayan da Tukur Buratai da ya sauka ya bayyana cewa a za kai nan da shekaru 20 ba za a iya magance Boko Haram ba.

Share.

game da Author