Yanzun nan Hukumar Kwallon Kafa ta Turai ta fitar da yadda gasar siri-daya-kwala ta ‘quarter final’ za ta kasance. Ga yadda aka hada sauran zaratan kungiyoyi 8 karo da junan su.
Man City vs Borussia Dortmund
Ko Man City zata iya tsallake siradin Dortmund ta kai ga wasan na kusa da karshe?
Wannan wasa dai sai an buga amma kuma an fi gani wa Man City nasara.
Porto vs Chelsea
Ita ma kungiyar Chelsea da zata kara da Porto, akwai kalubale a gabanta. Sai dai kuma da yake Kociyan ta tsohon hannu, zai iya banke Porto ya kai ga wasan kusa da na karshe.
Bayern Munich vs Paris Saint-Germain
Bayern za ta sake karawa da PSG a wasan Kwata-final. A wasan kakar bara, Bayern ta yi nasara akan PSG a wasan karshe inda ta yi lashe kofin a na wannan kakar kwallon kafa.
Real Madrid vs Liverpool
Ita ko Madrid za ta kara ne da Liverpool wanda ta taba karawa da ita a wasan karshe kuma ta yi nasara.
Wannan karon idan ta doke Liverpool ko kuma ita Liverpool din ta yi nasara zata kara da wanda yayi nasara ne a tsakanin Chelsea da Porto.
Haka ita ma Man City, idan ta yi nasara akan Dorrmund zata kara ne da kungiyar PSG ko Kuma Bayern a wasan kusa da na karshe, wanda duk za a buga su a cikinnwatan Afirilu.