Babbar Kotun Tarayya Abuja ta aza ranar 16 Ga Afrilu ta zama ranar da za ta yanke hukunci, dangane da karar da aka shigar, inda masu kara su ka kalubalanci karin wa’adin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Muhammad Adamu, bayan lokacin yin ritayar sa ya wuce, tun daga ranar 1 Ga Fabrairu, 2021.
Lauyan mai shigar da kara, Ugochukwu Ezekiel da kuma lauyan Sufeto Janar Adamu Alex Izinyon, sun shaida wa kotu a ranar Talata cewa kowa ya shirya sauraren karar.
Ezekiel ya ce, ya na rokon kotu ta yi nazari takardun da su ka gabatar domin amsa tambayoyin da wanda ya shigar da kara ya yi, a lokacin yanke hukuncin da Mai Shari’a zai yi.
Shi ma lauyan Sufeto Janar Adamu, mai suna Izinyon, wanda kuma babban lauya ne (SAN), ya tsaya kan bakan sa na nuna rashin amincewa da abubuwan da mai kara ya bijiro da su a gaban kotu.
PREMIUM TIMES ta buga labarin inda lauyoyin Adamu, Buhari da na Malami su ka shaida wa kotu cewa Sufeto Janar Adamu zai iya ci gaba da rike shugabancin rundunar ‘yan sandan Najeriya daga nan har 2023, ko ma 2024.
Wani lauya ne mai suna Maxwell Okpara ya shigar da karar kalubalantar wa’adin da Buhari ya kara wa Adamu bayan ya yi ritaya a ranar 1 Ga Fabrairu.
Lauyan ya ce Buhari ya dauki gatari ya faskara bisa kan ka’ida, don haka karin wa’adin haramtacce ne.
A kan haka ne ya roki kotu ta yi wancakali da Adamu daga kan kujerar shugabancin ’yan sanda da ya ke a kai.
Dama a ranar 9 Ga Maris, PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin wani cika-baki da Adamu ya yi inda ya ce “idan na ga dama ba zan sauka ba har sai 2023 ko 2024 .
A labarin, Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya shaida wa Babbar Kotun Tarayya cewa doka ta ba shi ikon ci gaba da zama Sufeto Janar har zuwa 2023 ko ma 2024.
Haka dai Babban Dan Sandan Najeriya din ya bayyana wa kotu, cikin wasu kwafen takardun da ya aika wa kotu.
Ya aika da kwafen takardun ne sakamakon karar sa da aka shigar a kutu, ana kalubalantar wa’adin watanni uku da Shugaba Muhammadu Buhari ya kara masa, bayan cikar wa’adin shekarun titayar sa, cikin watan Fabrairu, 2021.
A ranar Litinin dai Premium Times ta samu kwafen raddin wanda lauyan Sufeto Janar Adamu, mai suna Alex Izinyon ya gabatar wa kotu.
Ranar 1 Ga Fabrairu ce ya kamata a ce Adamu ya yi ritaya, amma kuma a ranar 3 Ga Fabrairu, sai Buhari ya kara masa wa’adin watanni uku.
To sai dai kuma daga cikin wadanda wannan wa’adi na wata uku da aka kara wa Adamu bai yi masu dadi ba, har da wani lauya mai zaman kan sa, mai suna Maxwell Opara.
Opara bai bar abin a cikin sa ba, sai ya garzaya kotu, inda ya shigar da Shugaba Buhari, Ministan Shari’a da Sufeto Janarar kara a kotu.
Opara ya shigar da kara cewa Sashe na 215 na Kundin Dokokin Najeriya da Sashe na 7 na Kundin Dokokin ’Yan Sanda ta shekarar 2020 duk sun haramta wa Adamu ci gaba da aikin dan sanda daga ranar 1 Ga Fabrairu, 2021.
‘Ni Wa’adi Na Bai Cika A Ranar 1 Ga Fabrairu Ba’ –IG Adamu
Adamu ya hakikice a kotu, ta hannun lauyan sa cewa shi dai wa’adin sa bai cika tun a ranar 1 Ga Fabrairu, 2021 ba.
Ya ce sabuwar Dokar Aikin Dan Sanda ta ba shi damar kara yin wasu shekaru hudu kan kujerar shugabancin ‘yan sanda Najeriya, har zuwa 2023 ko ma 2024.
Ya ce sabuwar doka ta rattaba cewa wa’adin sa ya fara ne tun daga 2019, lokacin da aka nada shi, har zuwa 2023. Ko kuma daga 2020 lokacin da aka kirkiro dokar zuwa 2024.
Adamu ya kara da nunin cewa ofishin sa duk da na aikin jami’in tsaro ne, amma ya na da burbushin siyasa, domin hadi ne aka yi masa, ba tsari ne na matakin aikin gwamnati ba.
Discussion about this post