Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya shaida wa Babbar Kotun Tarayya cewa doka ta ba shi ikon ci gaba da zama Sufeto Janar har zuwa 2023 ko ma 2024.
Haka dai Babban Dan Sandan Najeriya din ya bayyana wa kotu, cikin wasu kwafen takardun da ya aika wa kotu.
Ya aika da kwafen takardun ne sakamakon karar sa da aka shigar a kutu, ana kalubalantar wa’adin watanni uku da Shugaba Muhammadu Buhari ya kara masa, bayan cikar wa’adin shekarun titayar sa, cikin watan Fabrairu, 2021.
A ranar Litinin dai Premium Times ta samu kwafen raddin wanda lauyan Sufeto Janar Adamu, mai suna Alex Izinyon ya gabatar wa kotu.
Ranar 1 Ga Fabrairu ce ya kamata a ce Adamu ya yi ritaya, amma kuma a ranar 3 Ga Fabrairu, sai Buhari ya kara masa wa’adin watanni uku.
To sai dai kuma daga cikin wadanda wannan wa’adi na wata uku da aka kara wa Adamu bai yi masu dadi ba, har da wani lauya mai zaman kan sa, mai suna Maxwell Opara.
Opara bai bar abin a cikin sa ba, sai ya garzaya kotu, inda ya shigar da Shugaba Buhari, Ministan Shari’a da Sufeto Janarar kara a kotu.
Opara ya shigar da kara cewa Sashe na 215 na Kundin Dokokin Najeriya da Sashe na 7 na Kundin Dokokin ’Yan Sanda ta shekarar 2020 duk sun haramta wa Adamu ci gaba da aikin dan sanda daga ranar 1 Ga Fabrairu, 2021.
‘Ni Wa’adi Na Bai Cika A Ranar 1 Ga Fabrairu Ba’ –IG Adamu
Adamu ya hakikice a kotu, ta hannun lauyan sa cewa shi dai wa’adin sa bai cika tun a ranar 1 Ga Fabrairu, 2021 ba.
Ya ce sabuwar Dokar Aikin Dan Sanda ta ba shi damar kara yin wasu shekaru hudu kan kujerar shugabancin ‘yan sanda Najeriya, har zuwa 2023 ko ma 2024.
Ya ce sabuwar doka ta rattaba cewa wa’adin sa ya fara ne tun daga 2019, lokacin da aka nada shi, har zuwa 2023. Ko kuma daga 2020 lokacin da aka kirkiro dokar zuwa 2024.
Adamu ya kara da nunin cewa ofishin sa duk da na aikin jami’in tsaro ne, amma ya na da burbushin siyasa, domin hadi ne aka yi masa, ba tsari ne na matakin aikin gwamnati ba.
Discussion about this post