Kwamishinan Tsaro da Harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya bayyana a wata sanarwa cewa mahara sun kashe mutane har bakwai a hare-hare dabam dabam da su kai wasu kauyukan kananan hukumomin jihar Kaduna.
Aruwan ya ce hakan na kunshe ne a cikin rahoton da dakarun dake aikin samar da zaman lafiya da fatattakar yan bindiga a jihar suka aika wa gwamnati ranar Alhamis.
Wadanda wadanda maharan suka kashe sun hada da:
Wada Sulaiman
Amiru Saidu
Yusha’u Mohammadu
Osama Abdulwahab
Maharan sun kashe wadannan mutane ne a kauyen Gangi dake karamar hukumar Igabi.
Bayan haka sun babbake gidajen wasu mazauna kauyen uku.
Gidan Mohammad Jibril, gidan Salisu Ya’u da gidan Idris Muhammad sannan sun kona motar daukan kaya mallakin wani Umaru Saleh.
Sanarwar ta ce maharan sun tafi da shanun mutane har 20.
A karamar hukumar Igabi da Chikun ma an samu rahoton afka wa wasu ƙauyuka da ƴan bindigan suka yi.
A wadannan hare-hare ma an kashe mutane har biya sannan sun barnata dukiyoyin jama’a.
A karshe gwamna El-Rufai ya yaba wa sojojin da ke aikin kawo karshennrazjin tsaro a jihar sannan ya mika sakon ta’aziyyar sa ga iyalan waɗanda su rasa ƴan uwan su.
Discussion about this post