Gwamnan jihar Gombe Inuwa Yahaya ya sauya wa wasu kwamishinonin sa 6 wuraren ma’aikatu sannan ya sallami wasu kwamishinoni 3.
Yahaya ya mika sunayen wasu mutum uku ga majalisar dokokin jihar domin su tattance su saboda a maye gurbin kwamishinoni uku din da ya sallama.
Wadanda majalisar za ta tantance sun hada da Christopher Abdu, Buba Maisheru, Abdullahi Idris Kwami da Abubakar Aminu Musa.
Sakataren gwamnatin jihar Ibrahim Njodi ya sanar da haka a wani takarda da aka raba wa manema labarai ranar Litini.
Njodi ya ce kwamishinonin da aka canza wa wuraren aiki sun hada da kwamishinan ma’aikatar Filaye Mohammed Danladi Adamu inda aka maida shi Ma’aikatar Inganta yankin karkara, kwamishinan ilimi Habu Dahiru, Ma’aikatar kiwon lafiya, sannan kwamishinan inganta yankin karkara ma’aikatar Filaye.
Sannan kwamishinan matasa Julius Ishaya ya zama kwamishinan yada labarai, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida Dauda Batari Zambuk ya koma ma’aikatar Ilimi, kwamishinan gidaje da inganta birane Adamu Dishi Kupto ya ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida.
“Gwamnan ya kuma kori kwamishinan kiwon lafiya Ahmed Mohammed Gana, kwamishinan yada labarai Alhassan Ibrahim Kwami, da kwamishinan aiyuka na musamman, Mela Audu Nunghe.
“Kwamishinonin da aka kora za su mika ragamar mulki wa babban sakataren ma’aikatun su.
A karshe gwamna Inuwa ya godewa kwamishinonin da ya sallama yana mai yi musu fatan alkhairi.
Discussion about this post