Daya daga cikin daliban da aka ceto daga hannun’ yan bindiga a jihar Zamfara, Hafsat Anka ta shaida wa Kamfanin dillancin labaran Najeriya cewa maharan sun yi ta tsorata su da harbin bindiga a sama.
” Banda harbin bindiga da suka rika yi, sun rika ce mana duk wanda ya ne mi ya yi musu taurin kai za su yi gunduwa gunduwa da shi su soya su cinye shi tas.
Hafsat ta ce sun yi tafiya mai tsawon gaske kafin su isa maboyan ‘yan bindigan.
” Kwana daya tak da mu ka yi a dajin, ji muka yi kamar mun shekara ne a wurin.
Ta ce sun yi tafiya a ƙasa mai tsawo suna yi suna yada zango kafin har suka kai wurin da maharan suka ajiye su.
“Babu ruwan sha mai tsafta babu abincin kirki da aka ba mu mu ci sannan suna ta tsorata mu da karan bindiga.
“Mun zauna tare da maza ‘yan matasa sannan da wani babba da suke kira Kasalle ko yaya wanda ya hana matasan yi mana fyade.
“Maharan na sanye da kayan sojoji sannan sun rika cewa sun fi karfin jami’an tsaro shi yasa suka iya yin garkuwar da mu.
Hafsat ta ce za ta ci gaba da karatu sai dai wannan karon za ta zama ‘yar jeka ka dawo ne
Taron kwamitin tsaron kasa
Bayan kammala taron Kwamitin tsaro da aka yi a fadar shugaban Kasa ranar Talata, buhar ya saka tsauraran dokoki a jihar Zamfara domin fatattakar ‘Yan bindiga da suka sheke ayarsu a jihar da yankin Raewa maso Yamma.
Mai baiwa shugaban Kasa Shawara kan harkokin Tsaron Kasa, Babagana Monguno ne ya bayyana matsayar gwamnati a zantawa da manema labarai bayan taron.
” Daga yanzu ba a yardarwa wani jirgi yayi shawage ko ya ratsa ta sararin samaniyar jihar Zamfara ba, sannan kuma gwamnati ta hana ayyukan hako ma’adinai da ake yi a jihar.
Buhari ya ce” Ba za mu zuba ido, ana yi mana yadda aka so ba domin bata mana suna ta hanyar ayyukan hare-haren yan bindiga a kasar nan ba. Tura fa ta kai bango yanzu. Duk wanda ake zargi da hannu ko kuma ingiza tada zaune tsaye zai kuka da kansa.
” Duk wanda yake ganin shi shafaffe da mai ne zai rika ruruta wutar tada hankalin jama’a da hada wata alaka da ‘yan bindiga, dubun shi ya cika shi da’ yan bindigan yanzu zai.
Jihar Zamfara ta yi kaurin suna wajen ayyukan ‘yan bindiga a musamman yankin Arewa Maso Yamma.
Jihohin Kaduna da Katsina suma na fama da ire-iren wadannan hare-hare na’ Yan bindiga.
Da safiyar Talata ne aka sako daliban makarantar Mata dake Jangebe, Jihar Zamfara, bayan sun shafe kwanaki tsare a hannun ‘yan ta’adda.