Jami’an tsaro sun fatattaki yan bindiga a danin Kaduna, sun ceto mutum 8

0

Kakakin rundunar ‘Yan sandan jihar Kaduna Mohammed Jalige ya ya bayyana cewa jami’an tsaro dake aikin farautan yan bindiga sun fatattaki wasu yan bidiga da a karamar hukumar Giwa, dake jihar Kaduna.

Jami’ an tsaron sun yi wa maharan diran bazata ne inda maharan suka arce cikin daji har da yar da bindigar su daya kirar AK 47.

Ibrahim, Ede Gloria, Japheth Sani, Kinsley Edgbue, Anthony Okafor, Gabriel Agu, Chibuzo Nwokorie da Ifenyi Samuel Enugu.

Duk wadanda aka sace din sunce an waske dasu ne a titin Kano zuwa Zaria a hanyarsu na zuwa jihar Delta, a babban mota.

Gaba dayansu na asibiti ana duba su.

Share.

game da Author