Jami’an tsaro sun dakile harin ‘yan bindiga a makarantar Sakandaren Ikara, jihar Kaduna

0

Jami’an tsaro na sojoji da ‘yan sanda sun dakile kokarin farwa wata makarantar sakandaren kimiya da ke Ikara.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya bayyana haka a ganawa da yayi da manema labarai a Kaduna.

Aruwan ya ce daliban makarantan da yan banga ne suka sanar da jami’ an tsaro kokarin afkawa daliban su arce da su.

” Kafin su isa ga daliban jami’an tsaro da suka hada ‘Yan sanda, Sojoji da Yan sa kai suka fatattake su. Bayan haka an kirga yawan daliban da ke makarantan, an kuma gano dukkan su na nan babu wanda ya bace cikin su.

Bayan haka’yan bindiga sun yi kokarin afka wa rukunin gidajen manyan ma’aikata dake kusa da filin jirgin saman Kaduna, a nan ma sojojin saman Najeriya suka kawo musu dauki, suka fatattakesu ba tare da sun iya afka wa mutane ba.

Idan ba a manta ba sojoji sun ceto wasu dalibai da ma’aikatan makaranta raya gandun daji dake Kaduna 180 ranar Juma’a.

Akwai wasu 39 da har yanzu suna tsare a hannun ‘Yan bindiga.

‘ Yan binga suna neman a biya su kudin fansa naira miliyan 500 kafin su sako su.

Haka kuma a wani bidiyo da ya karade shafukan yanar gizo an nuna wasu daga cikin daliban da aka yi garkuwa da su a makarantar Forestry na kaduna ana tsatsaula musu bulala, suna rokon gwamnati ta biya yan bindigan su samu su koma gida.

Share.

game da Author