Kwamishinan Tsaro da Harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya bayyana cewa an ceto mutane 180 daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su a kwalejin koyar da ayyukan gona da raya gandun daji dake jihar Kaduna.
A bayanan da ke kunshe a sanarwar da Aruwan ya fitar bayan nasarar da jami’an tsaro suka samu wajen ceto wasu daga cikin ɗalibai da mutanen da mahara suka yi garkuwa ya ce har yanzu jami’an ysaro sun fantsama daji domin ceto sauran daliban.
” Maharan sun afka kwalejin koyar da ayyukan gona da raya gandun daji a Kaduna da karfe 11:30 na dare, ranar Alhamis.
“Maharan sun rusa wani sashe na katangar makarantar ne suka afka ciki sannan suka kwashe dalibai da malamai a makarantar.
Ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida ta samu labarin abin dake faruwa inda cikin gaggawa ta sanar wa sojoji.
“Daga cikin daliban da aka ceto akwai mata 42, maza 130, ma’aikatan makarantar 8 sannan har yanzu ba a san inda wasu mutum 30 suke ba.
“Wasu daga cikin wadanda aka ceto sun samu rauni, ana duba su a asibitin sojoji dake Kaduna.
Gwamna El-Rufai ya yaba wa sojojin da ke aikin kawo karshen rashin tsaro a jihar sannan ya yi adu’a Allah ya warkar da wadanda juka ji rauni a jikinsu.