Jama’atu ta umarci malaman da ke karkashin kungiyar su janye daga makabala da Abduljabbar

0

Jama’atu Nasril Islam ta umarci duka malaman da ke karkashin wannan kungiya kada su halarci makabalar da gwamnatin Kano ta shirya tsakanin malaman Kano da Sheikh Abduljabbar Kabara a Kano.

JNI ta bayyana wannan matsayi na ta a cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Kungiyar, Khalid Aliyu ya fitar, wadda ya aika wa PREMIUM TIMES ta hanyar sakon e-mel a ranar Alhamis.

Gwamnatin Jihar Kano dai ce ta shirya yin makabalar bayan da gamayyar malaman Izala, Salfiyyah, Tijjaniya da Qadiriyya su ka kai karar Abduljabbar ga Gwamna Abdullahi Ganduje.

Sun kai karar sa bisa zargin ya na tozarta wasu sahabbai da kuma yi wa wasu hadisan Annabi (SAW) baudaddiyar fahimta.

Dama malamin ya sha neman su zauna a yi makabala da malaman na Kano.

Bayan da Gwamna Ganduje ya hana shi karatu, tare da rufe masallacin sa da rushe makarantar sa, ya nemi a hada shi makabala da malaman, domin a ga wanda ke kan daidai da wanda ke kan kuskure a tsakanin su.

Sai dai kuma bayan Ganduje ya yi sanarwar amincewa a yi mawabala, sai wasu malaman Izala su ka rika cewa babu amfanin a yi zaman makabala da malamin, wanda ke kiran bangaren sa ‘Ashabil Kahfi War Raqeem’.

A Kano da sassan Arewacin kasar nan ana kiran mabiyan Abduljabbar ‘yan Kogo, su kuma gamayyar malaman Kano masu adawa da shi, ana kiran su ‘yan maja.

Cikin sanarwar da JNI ta fitar karkashin shugabancin Sarkin Musulmi Saad Abubakar, ta ce ” kungiyar bata goyon bayan wannan mukabala da gwamnatin jihar Kano ta shirya saboda babu abinda zai haifar sai dada nuna wa duniya ko wanene Abduljabbar da irin katobara da shishshigin da yake wa musulunci da izgilanci ga fiyayyen halitta”.

Sannan kuma sanarwar ta shawarci dukkan sauran malaman da ke da niyyar zuwa makabalar su canja tunani.

Sannan kuma sanarwar ta ce da Gwamna Abdullahi Ganduje ya shawarce su, da ba a shirya zaman makabala da Abduljabbar ba.

Kafin nan dai Sarkin Musulmi a baya ya yi murna da shirya makabalar, kuma ya ce da kan sa zai halarta, ba wakilci zai aika ba.

An dai shirya cewa za a yi wannan makabala a Fadar Sarkin Kano, Aminu Bayero a ranar 7 Ga Maris, 2021.

Yayin da shi ma Sheikh Ahmad Gumi bai goyi bayan a yi makabalar ba, haka Sheikh Aminu Daurawa da Sheikh Sani Rijiyar Lemo duk sun ba da usurun rashin damar halarta. Dalilin du kuwa shine, ” Da wanda ya san gaban sa a addini ake mukabala ba wanda iyakan sa falle daya ba, sai kuma hayagaga da yi wa addini shishshigi.

Share.

game da Author