IYA RUWA FIDDA KAI: ’Yan wasan Super Eagles sun lula Jamhuriyar Benin a karamin jirgin ruwa

0

’Yan wasan Super Eagles na Najeriya sun lula Jamhuriyar Benin mai makwautaka da Najeriya ta jirgin ruwa, domin karawa d kungiyar kwallon kafar kasar.

Sun shiga jirgin ruwa ne kasancewa babu tashin jirage tsakanin kasashen biyu a yanzu. Sannan kuma hanyar tafiya a mota ba ta da kyau, duk kuwa babu nisa sosai tsakanin kasashen biyu da su ka hada kan iyaka daya da juna.

Za su yi tafiyar awa daya da rabi (1:30) kafin su sauka daga jirgin ruwa su shiga Kwatano, babban birnin kasar.

Za a yi karawa tsakanin kungiyoyin biyu a birnin Porto-Novo (Kwatano), domin a karshe a gano a rukunin su wanda zai samu nasarar zuwa gasar cin Kofin Afrika, wanda za a yi a kasar Kamaru cikin shekara mai zuwa.

Shafin Football Epic News ya buga hotunan ’yan wasan a lokacin da su ke tafiya a cikin ruwa.

Share.

game da Author